
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Hukumar Jigilar Alhazan Nijeriya NAHCON, ta bada wa’adin zuwa ranar 8 ga watan Oktoba, 2025 ga hukumomin jigilar alhazai na jihohi da sauran ofisoshin lamuran aikin hajji da su bayyana adadin kuɗaɗen da maniyyatan 2026 za su biya.
A baya ne NAHCON ta sanar da kafin alƙalami na Naira miliyan 8.5 ga aikin hajjin 2026 a matsayin wani ɓangare na fara shirye-shirye akan lokaci.
A wata takarda da Daraktar labarai da hulɗa da jama’a ta NAHCON, Fatima Usara ta fitar a ranar Lahadi, ta bayyana cewa an bada wa’adin ne sakamakon fitar da jaddawalin ayyukan hajji da umara da Ma’aikatar Hajji da Umara ta Saudiyya ta fitar, wanda ke ƙunshe da dokoki masu tsauri.
Ta bayyana cewa, hukumomin Saudiyya sun ayyana 6 zuwa 23 ga Satumba, 2025 a matsayin lokacin shigar da ƴan kwangila cikin lamuran shirye-shirye da biyan kuɗaɗen Masha’ir yayin da 23 zuwa 24 kuma za a yi amfani da su wajen harkokin sufuri da masauki.
A cewar Shugaban hukumar, Farfesa Abdullahi Saleh Usman da kwamishinoni da Sakatarenta, Dakta Mustapha M. Ali zai tafi Saudiyya domin cimma matsaya akan yarjejeniyoyi da masu ruwa da tsaki.
