
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A kwanan nan ɗan gidan Sheikh Ahmad Gumi, wato Abdulrahman Ahmad ya kammala karatu a makarantar sojoji da ke Jihar Kaduna, NDA.
Tsohon Sanata, Shehu Sani ya tabbatar da haka a wani saƙo ta kafar X a ranar Lahadi, inda ya wallafa hoton ɗan tare da mahaifinsa.
A nan ya taya shi murna tare da masa fatan alkhairi da addu’o’i na gari yayin da ya fara aiki.
A da mahaifin nasa, Sheikh Gumi shi ma soja ne, inda har ta kai ga ya kai matsayin kyaftin kafin daga bisani ya yi murabus.
TheCable ta ruwaito cewa, hoton, wanda ake yaɗawa ya samo asali ne daga wani taro da aka yi gabanin su kammala karatun baki ɗaya.
Wata majiya ta ce, a ranar 29 ga watan Satumba za a yi bikin yaye su.
Saƙon, wanda tsohon sanatan ya wallafa yq janyo ra’ayoyi masu ban-ban da juna musamman a kafafen sadarwa duba da yadda Sheikh ke shiga tsakani wajen yin sulhu da ƴan bindiga da ɓangaren gwamnati.
Ga kaɗan daga ra’ayoyin wasu da jaridar IntelRegion ta ruwaito ta harshen Turanci:
“Okay…..now I understand why your government is reintegrating Boko Haram terrorists into the Nigerian military,” Aondona Onjefu, a netizen wrote.
“What a smart move by Gumi, bokoharam spokesperson/mediator has successfully planted his son in the Nigerian army. Do your arithmetic well, you will surely have the equal to =”, another user commented.
@Frankiee44 wrote; “Best wishes to the Nigerian army. Perhaps the son could be assigned to the troubled region, where he can demonstrate his courage just as well. After all, his father—the sheikh himself—has long been a voice for the people in that area…”
