Daga DAUDA USMAN a Legas
Shuwagabannin ɓangarorin kasuwar sayar da hatsi ta ƙaramar Hukumar Dandume dake cikin jihar Katsina a ƙarƙashin jagorancin Sarkin Kasuwar ta Dandume Alhaji Sama’ila Nalado, sun gudanar da taron haɗin kai tare da nemo hanyoyin da za su ƙaro cigaban kasuwar bakiɗaya.
Taron wanda suka saba yi a duk ƙarshen wata kuma ya gudana ne a harabar ofishin ƙungiyar ta dillalan buhunan hatsi na kasuwar ta ɗandume gabaɗaya.
Kaɗan daga cikin sunayen shuwagabannin ɓangarorin kasuwar ta sayar da hatsi a garin ɗandume sun haɗa da shi kansa Alhaji Rabiu Bagiyo wanda shine shugaban ƙungiyar masu dillancin buhunan hatsi a. kasuwar ta garin ɗandume da Shu’aibu Muktar sakataren kungiyar dillalan hatsi a kasuwar ta ɗandume da Yusuf Suleiman Zaki mai masaukin baƙin kasuwar sayar da hatsin ɗandume da Alhaji Ibrahim Usman Tero shugaban Rahama Dandume da mataimakin shugaban masu gumin shinkafa na kasuwar ɗandume.
Sauran sun haɗa da Alhaji Sani Chanaye mai masara ɗandume da Alhaji Magaji mai Masara Maikwama Dandume da Danjuma Abubakar shugaban ɓangaren busashen barkono Dandume da Umar Wada dillalin masara ɗandume da Alhaji Buhari mai alkama ɗandume da sauran manyan ‘yan kasuwar makamantansu inda shugaban ƙungiyar masu dillalancin buhunan masarar na Dangane Alhaji Rabiu Bagiyo a jawabin na taron ya fara da cewa a sakamakon ganin irin albarkatun nọman da Allah ya bai wa manoman arewacin Nijeriya suke ganin nan da ‘yan watanni kadan masu zuwa farashin kayan amfanin gona yana iya sakkowa kasa da yadda jama’a suke tunani.
Ya ce akan haka yake ganin ya kamata ya shawarci masu kuɗin ƙasar nan a cewarsa musamman masu bin manyan kasuwannin sayar da kayan amfanin gona na arewacin Nijeriya suna sayewa a hannun manoma su je su a jiye sai ya yi tsadar bala’i sannan su fito da shi domin sayar wa al’umma da su tausawa ‘yan Nijeriya a wajen wannan al’amari.
Ya cigaba da shawartar gwamnatin tarayyar Nijeriya da ta ƙara ƙoƙari a wajen samarwa manoman isashen takin zamani da maganin ƙwari a shekara mai zuwa domin manoman su noma wadataccen abincin da zai ishi Nijeriya har ƙasashen da suka yi makwabtaka da su cigaba da amfana sauran jawaban da suka gudana a wajen taron waɗanda suka fito daga bakunan sauran ‘yan kasuwar sakataren ƙungiyar ‘yan kasuwar Shu’aibu Muktar ɗandume da sauran waɗanda suka samu yin tsokaci a wajen taron dukkan jawaban su sun karkata ne wajen yin kiraye-kiraye ga gwamnatin tarayya da ta samarwa manoman isashen takin zamani a wannan shekarar mai zuwa sannan kuma ta ƙara ƙoƙari wajen kawo ƙarshen ta’addanci a Nijeriya domin manoman su saki jikinsu wajen noma abincin da Nijeriya take buƙata.
