NANS ta nesanta kanta daga zanga-zangar ƙungiyar ƙwadago

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Ƙungiyar Ɗaliban Najeriya (NANS) ta bayyana cewa ba za ta shiga zanga-zangar da ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya (NLC) ke shirin yi kan ƙarin farashin kira da intanet ba. A wani taron manema labarai da ta gudanar a Gombe, mataimakin shugaban NANS, Mu’azu Hina, ya ce manufar ƙungiyar ita ce kare muradun ɗalibai, ba shiga yajin aiki wanda ba ya da tasiri kai tsaye a kansu ba. Ya ce matsalolin da suka fi damun ɗalibai sun haɗa da ƙarancin kuɗin ilimi, rashin kayan more rayuwa, da matsalar tsaro a makarantu.

Hina ya jaddada cewa yin zanga-zanga ba shi ne mafita ga irin waɗannan matsaloli ba, yana mai nuna damuwa kan ingancin yunƙuri da NLC ke shirin yi. Ya bayyana yadda halin da tituna a Arewa maso Gabas suka shiga ke barazana ga rayuwar ɗalibai, musamman hanyar Numan-Yola-Gombe wacce ta haddasa asarar rayuka da dama. Ya buƙaci gwamnati da ta gaggauta gyara waɗannan tituna domin kare rayuwar al’umma, musamman ɗaliban da ke amfani da su.

A ƙarshe, NANS ta jaddada cewa tana kan bakanta na yin aiki tare da gwamnati ta hanyar tattaunawa don samun ingantattun kayayyakin more rayuwa, ƙarfafa tsaro, da kuma ƙara kuɗaɗen da ake ware wa fannin ilimi. Ƙungiyar ta ce a maimakon shiga zanga-zanga maras tasiri, ya fi dacewa a nemi hanyoyin da za su inganta rayuwar ɗaliban Najeriya.

By ukarofi