Nasarawa 2027: Magoya bayan Farfesa Haruna sun taro shi bayan dawowarsa daga ƙasar waje

Spread the love

Daga JOHN D WADA a Keffi

Ɗan takarar kujerar gwamnan jihar Nasarawa a inuwar jam’iyyar APC Farfesa Injiniya Mohammad Sani Haruna yace amincewa da manufofi da aƙidarsa ne yasa ɗimbin magoya bayansa suka fito ƙwansu da kwarkwata suka yi masa tarba ta musamman jim kaɗan da shigowarsa Najeriya daga ƙasar waje zuwa birnin Keffi ranar Litinin.

Farfesa Injiniya Mohammad Sani Haruna ya bayyana haka ne a lokacin da yake tattaunawa da ‘yan jarida jim kaɗan bayan wannan gagarumin tarba da ɗimbin magoya bayasa daga sassan jihar baki ɗaya suka yi masa.

Yace kasancewar a koyaushe yana tare da al’ummar nasa kuma tunda ya yanke shawarar fitowa takarar kujerar gwamnan jihar ta Nasarawa ne sai waɗannan magoya bayansa suka cigaba da ƙarfafa masa gwiwa bayan sunyi la’akari da ire-iren tsare-tsarensa da kyawawan manufofinsa ga jihar baki ɗaya idan Allah ya bashi nasara.

Yace tuni ya ɗauki matakin tabbatar ya dora daga inda gwamna Abdullahi Sule zai tsaya ta cigaba da gudanar da ayyukan cigaba da za su ɗaukaka sunan jihar a idon duniya baki ɗaya.

Ɗan takarar gwamnan jihar Nasarawar Farfesa Injiniya Mohammad Sani Haruna ya ƙara da cewa so yake idan ya samu dama yayi amfani da ƙwarewarsa da wayewarsa dangane da harkokin kimiya da fasahar zamani a nan gida Najeriya da ƙasar waje baki ɗaya wajen jawo wa jihar arziki ta jawo masu zuba jari daga ciki da wajen jihar a matakai daban-daban da haɓaka ɗimbin ma’adanai da Allah ya albarkaci jihar da su kamar yadda gwamna Abdullahi Sule ke yi a yanzu da uwa uba tabbatar da zaman lafiya a jihar baki ɗaya da sauransu.

Farfesa Injiniya Mohammad Sani Haruna ya kuma yaba wa sauran takwarorinsa ‘yan takaran gwamnan daga shiyar ta Yammacin jihar game da halin dattaku da suke nunawa kawo yanzu inda ya ƙara da cewa tuni dukansu ‘yan takaran gwamnan daga shiyar suka yi alƙawarin mara wa duk wanda Allah ya zaɓe shi daga cikinsu kana ya godewa waɗannan ɗimbin magoya bayansa da suka masa wannan karramawa ta musamman tare da fatan Allah ya komar dasu gidajensu lafiya.

Wasu manyan mutane dake tafiyar Farfesa Mohammad Sani Haruna din da wakilinmu ya gana dasu a yayin gangamin duk sun yaba wa kyawawan halayen ɗan takarar nasu inda suka ce sam basu yi mamakin irin yawan mutane da yawa musamman daga yankunan karkara suka fito da kansu suka nuna wa Farfesa Sani Haruna soyayya ba.

Wakilinmu a jihar ta Nasarawa John Dogo Wada ya kuma rubuto cewa waɗannan ɗimbin magoya bayan fitattan ɗan takarar gwamnan wato Injiniya Farfesa Mohammad Sani Haruna jin labarin shigowarsa Najeriya daga ƙasar waje inda ya je wani aiki a hukumance ke da wuya sai suka yi cincirindo daga garin Keffi zuwa Tudun-wada inda suka masa tarbar ta musamman sa’anan suka zaga dashi sassan yankin da cikin garin Keffi cikin farin ciki da annashuwa suna rera wakokin yabon gwanin nasu da sauransu.

By ukarofi