2026: JAMB ta sauya lokacin zuwa jarrabawar UTME ga ɗalibai

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumar kula da lamuran samar da gurbin karatu ga ɗalibai a manyan makarantu (JAMB), ta sanar da sauyi dangane da lokacin zuwa rubuta jarrabawar UTME ta 2026 ga ɗalibai musamman ‘yan sahun farko.

A wani saƙo da ta wallafa a shafinta na kafar X a ranar Litinin kamar yadda Manhaja ta ruwaito, JAMB ta ce a yanzu, ɗaliban za su halarci wuraren rubuta jarrabawar da aka tsara musu ne da misalin ƙarfe 7:00 na safe a madadin 6:30 da aka tsara da fari.

Haka kuma, za a fara rubuta jarrabawar ne da misalin ƙarfe 8:30 na safen sannan a kammala a 10:30, wato tsawon sa’o’i biyu kenan.

Hukumar ta ƙara da cewa, a yanzu babu buƙatar sai ɗalibai sun sake ciro takardar jarrabawarsu daga na’ura bayan sauyin da ta yi.

Cikakken jaddawalin jarrabawar ya ƙunshi zango huɗu da za a yi su daga ranar Litinin zuwa Juma’a, yayin ta yi wasu ‘yan gyare-gyare game da lokutan kowane zango domin tabbatar da gudanar da cibiyoyin jarrabawar na CBT a dukkan sassan Nijeriya.

Wannan mataki na zuwa ne a daidai lokacin da ƙorafe-ƙorafen ƙalubalen tafiyar sanyin safiya daga ɓangaren ɗalibai da iyaye suka yawaita yi, ciki har da damuwa akan tsaro a hanyoyi gabanin asubahi da kuma wahalhalun jigila ga masu zuwa daga wurare masu nisa.

An tsara gudanar da jarrabawar UTMEn ne daga ranar Alhamis, 16 zuwa 25 ga watan Afrilu, 2026.

By Babaji