Daga JOHN D WADA Lafia
Yayin da rikicin APC na jihar Nasarawa kan wanda za a zaɓa a matsayin ɗan takarar gwamna ya ƙara zurfafa inda tsohon gwamnan jihar Umaru Tanko Al-Makura ya ƙi bayyana a wajen taron zuba jari na gwamnatin jihar da Gwamna Abdullahi Sule ya shirya.
Wakilinmu da ya kasance a wajen taron ya gano cewa an shirya taron ne daga 6 zuwa 7 ga Mayu 2026 inda masu zuba jari da aka gayyata suke gabatar da kasidai akan hanyoyin faɗaɗa zuba jari a jihar yayin da mulkin Abdullahi Sule ke gab da kammaluwa.
Masu sharhi kan harkokin siyasa na ganin cewa kasancewar Al-Makura shi ne tsohon gwamnan da ya taimaka wa Gwamna Sule ya hau mulki ya kamata ya kasance a wurin taron domin taron ya shafi ci gaban jihar Nasarawar ne baki ɗaya musamman fannin tattalin arzikin ta.
Haka kuma an gano cewa kwanannan an danganta tsohon gwamnan da saɓani da Sule kan batun magajin gwamnan a 2027 musamman bayan gwamnan ya bayyana goyon bayansa ga Sanata Ahmed Wadada a matsayin magajinsa.
Rikicin ya ƙara tsananta ne bayan Al-Makura ya soki goyon bayan da gwamnan ya sanar ga Wadada din yana mai cewa ya yi gaggawa kuma ba a tattauna da shi da wasu jiga-jigan jihar kafin a ɗau matakin ba da hakan ya ƙara tsananta dangantaka tsakanin manyan jam’iyyar.
Amma Gwamna Sule a fitowarsa a wani gidan talabijin na ƙasa ya ƙalubalanci Al-Makura yana cewa biyayyarsa ga shi wata dama ce ba haƙƙi ba.
Duk da haka masu sharhi kan siyasa na ganin rashin halartar Al-Makura wata alama ce ta ƙara tsagewar tsarin cikin gida na APC a Nasarawa.
Da yake jawabi a taron zuba jari na 2026, Sule ya ce wannan shi ne taron zuba jari na ƙarshe a ƙarƙashin gwamnatinsa kuma lokaci ne mai matuƙar muhimmanci ga tafarkin tattalin arzikin jihar.
Ya bayyana shi a matsayin “dandali na dabarun da za a ƙara ƙarfafa nasarorin da aka samu da kuma tsara hanya ga sabon matakin ci gaban tattalin arziki.”
Ya tuna cewa taron “Diamond in the Rough” na 2022 ya gabatar da albarkatun ƙasa na Nasarawa da kusancinta da Abuja ga masu zuba jari, yayin da taron “Industrial Renaissance” na 2024 ya mayar da hankali kan noma, haƙar ma’adinai, masana’antu da ababen more rayuwa.
Taron na yanzu a cewarsa an tsara shi ne domin kiyaye da kafa sauye-sauye a cikin cibiyoyi masu ɗorewa domin ci gaba har bayan mulkin mutum ɗaya.
Amma a ƙarƙashin saƙon tattalin arziki, masu sharhi na cewa ɓangaren siyasa na ƙara bayyana: manyan ƙungiyoyi biyu a cikin APC na ƙara tsara kansu domin 2027, kuma halarta ko rashin halarta a manyan tarukan jihar yanzu ana ganin sa a matsayin saƙon siyasa.
A taƙaice dai rashin halartar Al-Makura a taron zuba jari na ƙarshe a gwamnatin Injiniya Abdullahi Sule ɗin ya ƙara dagula batun sasantawar tsakanin manyan ‘yan siyasan biyun masu faɗa-aji a jihar game da ainihin wanda ya dace ya gaji gwamnan a 2027.
