Nasarorin da na samu a harkar rubutu ba irin waɗanda sauran marubuta ke lissafawa ba ne – Tijjani Muhammad Musa

Spread the love

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

MANHAJA: Mu fara da jin cikakken sunanka?

ARC. TLIJANI: Cikakken sunana shi ne Arc. Tijjani Muhammad Tajuddin Musa. Ina yi wa kaina laƙabi da Muhammad Tajajjini. Wasu kuma da suka sanni tun muna yara ƙanana su kan kira ni da Tajo kai tsaye. Ni marubucin adabi ne kuma ina rubuce-rubucena cikin harsuna biyu wato Hausa da Turanci. Ina rubuta rubutattun waƙoƙi na Turanci da na Hausa da kuma rubutun zube. Har ila yau ni gogaggen ɗan Jarida ne, kuma cikakken mamba na Ƙungiyar Ƙwararrun ‘Yan Jarida a fannin rediyo da talabijin wato SNB. Sannan na samo asali daga tsatson zuriyar Gidan Sarkin Askan Basirka ne dake Ƙaramar Hukumar Gwaram a Jihar Jigawa. Magidanci ne ni mai y’ay’a maza da mata, sannan ina zaune ne a Birnin Kano.

Ko za ka gaya mana wani abu daga tarihin rayuwarka?

To, kamar yadda aka saba bisa aľadar ‘ya’yan musulmi, na fara karatuna ne a makarantar allo ta Marigayi Malam Shu’aibu Ali dake Gwagwarwa Birged, sannan daga baya na shiga ta zamani wato Gwagwarwa Firamare dake titin Airport. Sai na yi karatun gaba da firamare, inda na soma a Kano Teachers College (KTC) kenan, amma na kammala a Makarantar Gwamnati ta Kawaji dake Dakata.

Na yi karatu mai zurfi har zuwa digiri na biyu, wanda ake cewa digirin digirgir (M.Sc.) a fannin zana taswirar gidaje da mahalli wato Architecture a Jami’ar Ahmadu Bello ta Zaria, inda na kammala a shekarar 1998. Sannan a yanzu haka ina wani karatun na daban a matakin digiri na biyu (M.Sc.) shi kuma a fannin aikin jarida wato Mass Communication a Jami’ar Bayero ta Kano.

Kaɗan daga cikin tarihina a fagen aiki kuma shi ne da ni aka buɗe gidan rediyo mai watsa shirye-shirye a zangon FM na farko a Arewacin Nijeriya, wato Radio Kano 2 a 1989. Sannan da ni aka buɗe gidan rediyon farko mai zaman kansa wato Freedom Radio a shekarar 2003, inda muka tallafa wajen rainon tashar har aka kai gaci.

Na taɓa zama Shugaban Ƙungiyar Marubuta ta Nijeriya (ANA) reshen Jihar Kano a shekara ta 2021 zuwa 2023 bayan na zama Sakatarenta a 2017 zuwa 2021. Na kuma yi tafiye-tafiye don wakiltar ƙungiyar a wurare da dama.

A fagen wallafa kuma na fitar da littattafai guda uku kawo yanzu, biyu cikin harshen Turanci wanda suka haɗa da ‘The First Cup’ da ya ƙunshi waƙƙoƙina wajen 124 cikin harshen Turanci. Sai kuma ’30 Questions in 30 Days’ wanda wasu tambayoyi ne guda 30 da na yi cikin kwanaki 30 na watan Ramadana na shekarar 1431 (2010) bayan Hijira a shafina na Fesbuk. Sai kuma littafina na baya-bayan nan wato Sunayen Allah 99 da na rubuta shi da sigar sabon salon adabi na Hausa wato Halku da Hausa wanda da babu shi, amma Allah (SWT) cikin ikonSa da yardarSa na shigo mana da shi a karon farko.

Waɗannan na daga cikin litattafai wajen guda ashirin da na rubuta a fannoni daban-daban na rayuwa.

Daga cikin sauran akwai wasu guda uku da suka shafi fannin Zamantakewar Aure (Hausa) Gajerun Labarai (Turanci) sai kuma na Hausa Haiku Mai Carbi wanda suke dab da fitowa kasuwa in sha Allah.

A wani ɓangare na rayuwata kuma ni ne na kafa Gidauniyar Kwandala Foundation tare wasu bayin Allah da ra’ayinmu ya zo ɗaya a shekara ta 2005, wato shekaru ashirin kenan da suka wuce don taimakon mabuƙata. Kuma cikin waɗannan shekarun babu abin da muka dinga yi illa taimakon mutanen da suka tsinci kansu a cikin halin ƙaƙanakayi.

A fagen alki da sana’a kuwa ina daga cikin wadanda muka kafa kamfanin sadarwa mal suna SoundWord & Sight Communications masu ƙirƙiro wa kafafen sadarwa shirye-shirye, tallace-tallace, rubuce-rubuce da ma bidiyo kalakala wato “contents” ke nan don isar da saƙonni a jaridu, radiyo, talabijin, soshal midiya da ma dandalolin waɗannan kafafe a yanar gizo.

Bayan da wannan, mu ne masu mujallar online DesignWorld International (DWi) da SWS.Comms online Radio Ragaɗaɗau da SWS.Comms TV wanda nake shugabantar kamfanin. Hakazalika mu ne masu shafin nan na kyautata zamanzakewar aure wato ‘The Marriage Academy’ dake dandalin sada zumunta na Fesbuk.

Wanne abu ne ya fi tsaya maka a rai tun tasowarka da ba za ka manta shi ba?

Abubuwa biyu ne zuwa uku suka fi tsaya min a rai da ba zan manta da su ba a rayuwata.

Na ɗaya hana ni karanta Turanci a lokacin da na gama sakandire wanda babban burina a lokacin bai fi in koyl Turanci in dinga karanta labarai a talabijin ba musamman a NTA. Suna birge ni ba kaɗan ba. Amma aka ce da ni a’a, kwas ɗin kimiyya zan karanta tun da a gidanmu an samu wani a fagen karatun digiri yana Bayero yana karantar ilimin siyasa. Haka na hakura na je na karanta Architecture. Duk da shike ba na takaici akan al’armarin, amma abu ne da ba haka na so ba da farko. Sai daga baya da na ga hakan bai hana ni sarrafa harshen Turancin a magance ko a rubuce ko a kafofin sadarwa ba.

Sai abu na biyu. Ina matashi na so in shiga harkar kasuwanci na saye da sayar da sutura har ta kai ga na je ni Ikko don gano sirrin sayen kaya daga can Legas in dinga kawo dilar su Kano ina sayarwa. Rashin jari na N2,000 rak ya hana ni yi kuma a nan ma manyana suka ce in mai da hankali kan karatuna ba neman kuɗi ba. Nan ma na haƙura na bi shawarari iyayena.

Abu na uku kuwa wani abu ne na musamman da har gobe yana matuƙar faranta min rai da ba ni mamaki. Wannan al’amari ya faru ne lokacin da na je ni Makkah a karo na farko aikin Hajji. Akwai wata rana cikin kwanakin da muka yi bayan kammala sallar Magariba zuwa Isha’i an idar da sallah ina cikin farfajiyar Masallacin Ka’abah na tsaya ina addu’a ga Allah SWT don yi maSa godiya akan ni’imomin da ya yi mun a rayuwata da ba za su ƙirgu ko su misaltu ba.

Can ina cikin waɗannan addu’o’i sai wata tambaya ta faɗo min a zuciyata na tambayi Allah Azza Wa Jallah cewa, “Yanzu a duniyar nan in ba Kai ba wa ya isa ya kawo ni nan gaban dakin Ka’aba har in kasance cikin wannan ni’ima? Waye yake so ko ƙaunata har ta kai da zai fid da kuɗinsa ya ce, “Tajo, zo na biya maka kujerar Makkah tashi ka je ka sauke farali?” Na laluba na duba na ga wAllahil Azimu babu! Duk duniya ƙarƙaf ban gan shi ba, ban ga wanda ya yi kama da shi ba. Sai kawai na fashe da kuka wi-wi hawaye sharɓe-sharɓe, Na kuwa saki jiki sai yi nake mutane a kusa da ni ganin haka suka kama mamaki.

Da ƙyar na share hawayena na tafi daga wajen ina ta shisshiɗa kamar wani yaro ƙarami. A nan na san Allah SWT Yana matuƙar sona wAllahi Yana ƙaunata ba kaɗan ba. Don haka na samu natsuwa na daina damuwa da dukkan wata ƙiyayyar ta mutane. Tun da Allah (AWJ) Ya kai ni Makkah da Madinah na yi aikin Hajji na yi ziyara ga Manzona (SAWS), ina dan talaka futik maras gata maras galihu ai Ubangijina Ya gama yi mun komai. Ka ji abubuwan da suke yawan tsayamun a raina.

Me ya canza a tunaninka dangane da yadda ka ke kallon rayuwa a da can baya da yanzu da ka fara manyanta?

A gaskiya akwai abubuwa da yawa da suka canja a rayuwar da in an kwatanta da ta yanzu. Babba daga ciki babu irin yadda lokaci yake gudu yanzu wato Jumma’a zuwa Jumma’a ta kasance kamar kwana ɗaya ne rak a tsakanin su. Haka kewayowar watan Ramadan zuwa wani Ramadan ɗin kai ka ce wata uku be kacal tsakanin su wanda da ba haka ba ne.

Na biyu rashin gaskiya da tsoron Allah ya zama kamar mutane da yawa ba su yarda da ranar tashin alƙiyama ba. Don za ka ga wasu aika-aikan da ake yi yanzu sam ba za ka ga wani ko wata na kawo gamuwarsu da Allah cikin lamuransu ba. Na uku lalacewar neman ilimi da amfani da shi. Da za ka ga masu karatu suna jin jiki wajen neman ilimi amma ban da yau. Satar amsa ko ba da wani abu don samun sakamakon jarabawa mai kyau ya zama ruwan dare. Wannan al’amari bai tsaya akan ilimi kawai ba yanzu ya hau kan kusan komai.

Na hudu akwai lalacewar zamantakewar aure gami da tarbiyyar yara duk sun zama abin da suka zama. Na biyar ga lalaci ya yi wa matasanmu da yawa katutu ba sa son yin aiki ko koyon sana’a. Ga su da son su samu maƙudan kuɗi cikin ɗan lokaci kankani.

Waɗanne abubuwa ne suke burge ka a rayuwa?

Abubuwan na da yawa. Daga cikin su a hayatad duniya akwai yin gaskiya da riƙon amana da cika alƙawari. Akwai haƙuri da ƙanƙan da kai da girmama na gaba ga ladabi da biyayya. Ina kuma son rashin karaya da rashin jin tsoro da jajircewa da imani da cewa mutum zai ci nasara ta hanyar da ta dace akan abin da ya ƙudiri niyyar samu. Sai kuma fafutuka da dagewa wajen neman na kai da tawakkali da dai sauransu.

Yaya ka tsinci kanka a fagen rubuce-rubuce da ƙirƙira?

To, ni dai tun ina yaro ƙarami akwai ni da lura da abubuwan dake faruwa a tattare da ni. Ga yawan tambaye-tambaye har ta kai mahaifiyata kan amsa mun wasu tambayoyi na da “Idon Matambayi,” idan na ishe ta da tambaya. Tun ban gane me take nufi ba har na zo na gano sai in rabu da ita sai na sake dawowa a wani karon.

To, da na zo na iya karatu da rubutu na kan gudanar da bincike a littattafai ko in tambayi yayyena da suka fi ni ilimi. Wani abin in ɗauka a ka wani kuma sai na rubuta shi don gudun mantuwa. A hankali sai abokaina suka fara ce na cika ƙwaƙule-ƙwaƙule, in kuma na yi magana wasu sai su ce abin ya ba da ma’ana.

To, sai ta kasance na kan rubuta wasu daga cikin tunanina cikin littattafaina don kar su bace min daga baya. A hankali a hankali sai suka soma taruwa. Daga bisani sai na soma hada jimla da jimla har sakin layi ya soma fitowa. Wasu yayyena in suka karanta rubutuna sai su ce yaushe ka iya rubuta waƙar Turanci wato poem ke nan alhali ni ban ma san ta ya ake rubuta wata waƙa ba. Ni dai kawai ta mahaukaci nake da ya ce “Ahaf, kanku ake ji ni dai wanka na nake yi.”

To, ka ji ta yadda na tsinci kaina a marubucin waƙoƙin Turanci ke nan. Amma fa waƙar Hausa ban soma rubuta ta ba sai da na zama mutum magidanci don duka-duka har yanzu ban kai shekaru 10 da na fara rubuta ta ba. Kuma dalilin fita kunya ce ta sa ni koyonta kuma na soma rubuta ta.

Sannan da Ballagaza na fara ta, amma yanzu da yardar Allah da koyarwar malamaina da karanta littattafan koyar da yadda ake rubuta waƙoƙin Hausa alhamdulillah na soma kamo bakin zaren. Amma har yanzu a gaskiya ban uya ta ba don da saura na ba kaɗan ba.

Ban da rubutun waƙoƙi da na zube, ko akwai wani ɓangare na adabi da ka ke sha’awar ba da gudummawa?

Tabbas akwai, don na iya rubutun wasan kwaikwayo wato dirama ko finafinai har ma ina da wasu sikirif na fim da na rubuta. Amma da yake ba ni da sha’awar harkar finafinai, waɗannan sikirif biyu zuwa uku na nan a ajiye ba na ta tasu. Ban da wannan kuma da shi ke muna harkar tallace-tallace a kafafen sadarwa na dauri da sabo na zamani musamman gidajen radiyo da soshal midiya haka ta sa akan nemi mu ƙirƙiri sikirif na gajeren wasan kwaikwayo, yadda za a tallata hajjoji da kayayyakin kamfanoni ko isar da saƙonnin hukumomi da cibiyoyi manya-manya. Sannan akwai ƙungiyoyi na duniya masu zaman kansu irin su Majalisar Ɗinkin Duniya (UN), Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), Hukumar Majalisar Ɗinkin Duniya kan Ilimi da Ƙananan Yara (UNESCO) da USAID da ire-irensu.

Akwai kuma harkar fassara daga harsuna daban-daban zuwa wasu harsunan da shi ma ke buƙatar masu harkar rubuce-rubuce su aiwatar. Ta haka ko shakka babu ma’abota adabi mu kan ba da gudummawarmu ba kaɗan ba.

Waɗanne nasarori ka samu da za ka yi alfahari da su a harkar rubutu?

Ni nasarorin da na samu a harkar rubutu ba irin waɗanda sauran marubuta ko mutane suke lissafawa a harkar rubuce-rubuce ba ne, duk da shi ke ina da ire-irensu da dama. Amma ni babban abin alfaharina bai wuce samun nasarar wallafa littafina na ‘Sunayen Allah 99 – Hausa Haiku’ ba. Don wannan burin na daga cikin abin da na roƙi Allah na kuma dinga roƙon Sa da ya ba ni aron rai da lafiya gami da wadatar in rubuta shi in kammala shi in wallafa shi yadda na so shi da ingancinsa da kyautata masa kamanni da siffa. Kuma alhamdulillah don kwalliya ta biya kuɗin sabulu.

Ni dai tun da Ubangijina Allah Ya yardar mun buga littafin nan ta wannan sabon salon ta hannuna wanda a da babu irinsa a adabin Hausa sai yanzu, ai ni Allah Ar-Razzaƙu Ya gama yi mun komai na arziki a duniya. Sauran nasarorina na da da na yanzu da wanda za su zo nan gaba in sha Allah duk za su kasance kamar gyara ne akan wannan.

Za mu ci gaba

By ukarofi