Daga UMAR GARBA a Katsina
Wata mata mai juna biyu, Aisha Najamu, ta rasa ranta a asibitin Turai Umaru Musa Yar’Adua da ke Katsina bayan ma’aikatan asibitin sun ƙi karɓar kuɗin iskar ‘oxygen’ ta hanyar tura kuɗi ta yanbar gizo (wato transfer), inda suka dage cewa sai an biya kuɗi a hannu (cash) kafin a ba ta agajin gaggawa. Hakan ya sa matar har ta mutu, bisa jinkirin saka mata iskar da asibitin ta ƙi yi, don ba su zo da kuɗi a hannu ba.
Lamarin, wanda ya faru ne a ranar Laraba da daddare, shaidun gani da ido sun shaida wa kafar labarai ta Katsina Times cewa, matar ta zo asibitin ne a cikin mawuyacin hali tana buƙatar iskar numfashi da gaggawa, amma mai karɓar kuɗi ya ƙi aiwatar da biyan kuɗin, saboda ba ta da kuɗi a hannu. Ma’aikacin ya dage kan cewa, dokar asibitin ta haramta karɓar ‘transfer’.
Wani mutum da ya shiga tsakani ya ce, ya roƙi ma’aikacin da ya karɓi ‘transfer’, domin a ceto rayuwar matar, amma ma’aikacin ya nace kan cewa, ba zai karya dokar asibiti ba. Mutumin ya ce, har ya yi masa tayin ɗaukar dukkan kuɗin ya kuma yi tayin ƙara masa kuɗi akai, ta hanyar yi masa ‘transfer’, saboda shi ma ba shi da ‘cash’, ƙarshe dai har ya yi masa tayin kuɗi Dala 100, don ya karɓa ya ceto matar, amma ma’aikacin ya ƙi yarda.
A daidai lokacin da ake ta fafutukar neman tsabar kuɗi, majiyarmu ta ce Aisha tana ta kuka tana roƙon a taimaka mata, amma kafin a samu mafita ta rasu a lokacin da ta ke neman agaji.
Majiyar Blueprint Manhaja ta Katsina Times ta tuntuɓi hukumar asibitin Turai Umaru Musa Yar’Adua, sun ce ba su samu ƙorafi daga jama’a ba sai na ƙungiyar kare haƙƙin ɗan Adam ta IHRAAC.
Wakilin manajan asibitin, Aminu Ibrahim ƙofar Bai, ya jajenta wa iyalan da lamarin ya shafa ya kuma tabbatar da cewa, za su ziyarci iyalan marigayiyar tare da binciken duk wani ma’aikacin da ya yi sakaci a aikinsa.
Asibitin ya kare kansa da cewa, tsarin gwamnatin Katsina da ake kira ‘TSA’ ne ya hana karɓar ‘transfer’ kuma ba su da ‘POS’ da za a iya amfani da shi. Sun kuma koka da ƙarancin iskar ‘oɗygen’, inda suka ce daga Daura kawai suke iya samo ta.
Shugaban ɓangaren Haɗa Magunguna na Asibitin, Perm. Usman Salisu Wada, ya ce, ma’aikacin da ya ƙi karɓar ‘transfer’ “yana tsananin bin doka ne”, saboda tsoron dakatarwa. Ya ƙara da cewa, wasu marasa lafiya da ake ɗaga wa ƙafar lamuni, sukan tafi bayan an sallame su ba tare da sun biya kuɗin ba.
