Matawalle ba tsararka ba ne – APC ga Gwamna Dauda

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Jam’iyyar APC ta Jihar Zamfara ya yi Allah wadai da sanarwar da Gwamna Dauda Lawal ya yi a kafafen yaɗa labarai kwanan nan da ake zargin ya bai wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu sharaɗin ya kori ƙaramin ministan tsaro, Hon. Bello Mohammed Matawalle kafin ya koma jam’iyyar ta APC.

Sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar Yusuf Idris ya yi wannan sanarwar a cikin wata sanarwa da ya fitar wa manema labarai a Gusau a yau Alhamis.

Jam’iyyar ta yi Allah wadai da yadda Gwamna Dauda ya ya ɗauki Matawalle a matsayin babban abokin gabar sa da kuma hamayyar siyasa a duk duniya, tana mai jaddada cewa siyasar Matawalle ba ta da kwatankwaci a tsakanin sabbin shiga jam’iyyar ta APC kamar Gwamna Dauda.

Jam’iyyar ta koka da yadda Gwamna Dauda ya yi yunƙurin yin Allah wadai da duk wani kyakkyawan ƙoƙarin da Matawalle ke yi don tabbatar da zaman lafiya a dukkan sassan ƙasar ta hanyar yin kira ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya cire shi.

A cewar sanarwar, tun da daɗewa, gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, yana ɓoye-ɓoye ga mutanensa a jam’iyyar PDP mai mulki a jihar yayin da yake neman canza sheka a gefe ɗaya yana roƙon a karɓe shi cikin APC.

“Abin mamaki ne matuƙar gaske, bisa yadda Gwamna Dauda Lawal ya fito fili yana gindaya sharuɗɗa kan yadda zai shiga APC da zarar Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kori Matawalle”.

“Matawalle ya fi dacewa da siyasa fiye da Gwamna Dauda Lawal wanda ‘yan jam’iyyarsa ke gujewa zuwa APC ta hanyar ƙoƙarin Matawalle.”

Jam’iyyar ta umarci gwamnan da ya bi hanyar da ta dace ta hanyar samun shugabannin jam’iyyar na jihar ya bayyana amincewar sa zai bar Jam’iyyar sa ya dawo APC don a karɓe shi.

“Gwamna Dauda kuma zai iya farawa ta hanyar sakin ‘yan APC 270 marasa laifi waɗanda ya tsare saboda kawai ‘yan APC ne Kafin mu aminta ya dawo APC .” Jam’iyyar ta ce

By ukarofi