NASENI ta bada tallafin miliyan N70.5 ga injiniyoyi mata shida

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Hukumar kula da Kayayyakin Kimiyya da Injiniya ta ƙasa NASENI ta hannun kwamitin shugaban ƙasa kan canjin fasaha ta PICTT ta ba da tallafin Naira miliyan 70.5 ga injiniyoyi mata shida.

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labarai na NASENI, Olusegun Ayeoyenikan, ya fitar ranar Laraba a Abuja.

Mista Ayeoyenikan ya ce an bayar da tallafin ne ga mutane shida da suka yi nasara a ƙarƙashin shirin Deɓeloping Engineering Leaders through Her (DELT-Her), tare da gabatar da shawarwarin da aka ƙaddamar a matsayin wani ɓangare na shirin NASENI na Delta-2.

Ya ƙara da cewa, a ranar 8 ga Maris, hukumar ta ɓullo da shirin DELT-Her, da nufin magance matsalar rashin daidaiton jinsi a harkokin kasuwanci na injiniya da fasaha a Nijeriya.

Mataimakin Shugaban Hukumar NASENI, Khalil Halilu, wanda Daraktan Gudanarwa na Tsare-tsare da Cigaban Kasuwanci, Dokta Nonyem Onyechi ya wakilta, ya bayyana cewa shirin na DELT-Her na neman ƙarfafawa mata matasa aikin injiniya da fasaha.

Ya kuma jaddada muhimmancin samar wa mata kayayyakin aiki, dandali, da tallafi don yin fice a fagagen da maza suka mamaye.

“Ina ƙarfafa wa waɗanda aka karrama ƙwarin gwiwar ganin nasarar da suka samu a matsayin fitila ga wasu da kuma jajircewa wajen bunƙasa muhallin da mata za su iya bunƙasa a fannin injiniya da fasaha,” inji Halilu.

Shugaban PICTT, Dr Mohammed Dahiru, ya ce bayan tantance aikace-aikacen sama da 120, an zaɓi sabbin ayyuka guda shida don samar da kuɗaɗe, tare da karɓar tallafi, tallafin fasaha, da haɗin gwiwar abokan hulɗa don kasuwanci.

Mista Dahiru ya ƙara da cewa, an kuma zaɓo wasu daga cikin waɗanda aka karrama domin halartar taron shekara-shekara na AFRI da za a yi a birnin Cape Town na ƙasar Afirka ta Kudu, bisa la’akari da ayyukan da suka yi.

By ukarofi