
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Masu ruwa da tsaki a fannin ilimi sun sake sukar Cibiyar Gudanar da Jarrabawa ta Yammacin Afirka (WAEC) bisa sauya sakamakon jarrabawar WASSCE ta 2025.
Rahotanni sun bayyana cewa masu ruwa da tsakin a mabanbanta hira da kamfanin dillancin labarai (NAN) a Abuja, sun nemi a yi bincike mai zurfin akan baki ɗaya hukumar gudanarwar WAEC.
Sun ce, ba za a amince da samun kurakurai a jarrabawar kammala sakandare ta ɗalibai ba duba da cewa shi ne abinda zai nuna cancantar su shiga makarantun gaba.
Haka kuma, sun bayyana cewa matuƙar za a riƙa samun irin haka a manyan jarrabawa, to za a yi wa ƙwarewar Nijeriya ta fuskar ilimi illa a cikin gida da waje.
A ranar 4 ga Yuli, 2025 WAEC ta fitar da sakamakon inda kaso 38.32 na ɗalibai 1,969,313 da suka rubuta jarrabawar ne kaɗai suka samu kiredit biyar ko sama da haka ciki har da darussan Turanci da Lissafi.
Lamarin da ya janyo cecekuce da suka daga iyaye da ƙungiyoyin al’umma inda suka yi ta kiraye-kirayen a soke sakamakon takardun musamman na Turanci da Lissafi.
Daga bisani WAEC ta ce ta gano an samu tsaiko ne a harkar sadarwa yayin gudanar da nazari akan sakamakon, wanda ya sa ta rufe shafin dubawa.
Baya ga haka ne ta sake buɗe shafin a ranar Juma’a, inda aka ga matakin nasarar ya haura zuwa kaso 62.96, wato ruɓi biyu na wanda aka fitar da fari.
