Filato: Jami’an tsaro sun kama sojan bogi a Jos

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Jami’an sojojin Atisayen SAFE HEAVEN, wato OPSH a Filato, sun yi nasarar kama wani Musa Ali a Jos bisa laifin sojan gona, inda ya yi basaja a matsayin jami’insu.

Kakakin jami’an, Manjo Samson Zhakom ya faɗi haka a wata sanarwa da ya fitar a Jos, Babban Birnin Jihar Filato, ranar Asabar.

Ya ce, an yi nasarar kama wanda ake zargin ne a yayin da ya yi yunƙurin damfarar wasu jama’an gari.

Musamman Kakakin ya ce wanda ake zargin ya yi yunƙurin damfarar iyalan wani mai safarar makamai da aka kama da sunan zai musu hanya a fito da shi.

Akan haka ne ya karɓi N400,000 daga gare su wanda a halin yanzu ake gudanar da bincike akansa, inda ya faɗa musu cewa, zai bi wasu hanyoyi domin ganin an dakatar da binciken.

Manjo Zhakom ya kuma ce, za a yi bincike mai zurfi akan sa tare da ɗaukar matakin da ya dace da laifin da ya aikata, yana mai kira ga al’umma da su cigaba da kasancewa masu lura da ababen da ke kai kawo acikinsu.

By Babaji