Ɗakin karatun Obasanjo ya zargi EFCC da kutse ba bisa doka ba

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumar Gudanarwar Ɗakin Karatu ta Obasanjo da ke Abeokuta a Jihar Ogun, ta soki Hukumar EFCC bisa yi mata kutse a farfajiyarta.

Ta ce, hakan saɓa wa doka ne na baƙi yayin da suke tsaka da taro a safiyar ranar Lahadi.

Jami’an hukumar yayin wani samame, sun kama wasu da ake zargin ƴan yahoo ne a otal ɗin Green Legacy da ke farfajiyar ɗakin karatun, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Da ya ke magana kan al’amarin, mai taimaka wa tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo kan harkar yaɗa labarai, Kayode Adeyemi ya bayyana hakan a matsayin kutse ga kayan sirri.

Ya ce, matakin na EFCC take ƴanci ne ga waɗanda suka taru a yayin gudanar taron.

Ya kuma ce, kimanin jami’ai 50 ne suka yi ikirarin ƴan EFCC ne su ƙarƙashin jagorancin wani mai suna Olapade yayin da suka yi wa farfajiyar diran mikiya.

Ya kuma nemi a yi musu bayani game da matakin tare da bada haƙuri ga baki ɗaya waɗanda abin ya shafa ciki har da waɗanda aka raunata yayin hayaniya da harbe-harbe da aka samu a lokacin da abin ya faru.

By Babaji