TETFUND ta ware Naira miliyan 100,000 don bunƙasa ilimin likitanci a manyan makarantu

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Asusun kula da manyan makarantu na ƙasa (TETFUND) ya saki sama da Naira biliyan 100 ga manyan makarantun ƙasar nan a matsayin tallafin inganta ilimin likitanci da unguwar zoma da makamantansu domin ƙara yawan ma’aikatan kiwon lafiya a ƙasar nan.

Shugaban asusun na TETFUND, Rt. Hon Aminu Bello Masari, ya bayyana haka a wata tattaunawa da yayi da manema labarai a Katsina.

Ya ce yin hakan manufa ce ta shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu na ganin an shawo kan matsalar ƙarancin ma’aikata a fannin kiwon lafiya, duba da yadda likitoci da malaman jinya da sauran ƙwararru a fannin kiwon lafiya suka yi ta barin ƙasar nan a ‘yan shekarun baya.

“Shugaban ƙasa ya damu matuƙa da yadda likitoci da sauran ƙwararru a fannin kiwon lafiya suka yi ta barin ƙasar da kuma yadda lamarin ke shafar ɓangaren kiwon lafiya, wannan tallafin na cikin ƙudurorin sa na ganin cewa an cike giɓin da aka samu a wannan fannin.

“An zaɓo manyan makarantu guda uku a kowace shiyya a ƙasar nan, cikin shiyyoyi shida da muke da su, kowace makaranta za ta samu Naira biliyan huɗu don gudanar da ayyuka da za su ƙara yawan ɗaliban da za su riƙa ɗauka suna horar da su a fannin ilimin likitanci da jinya da ilimin magunguna na zamani da sauransu.

“Manufar ita ce a ruɓanya adadin likitoci da ma’aikatan jinya da masu ilimin haɗa magunguna a ƙasar nan, wannan ko shakka babu zai inganta harkar kiwon lafiya a ƙasar nan.

“Kowace shekara hukumar TETFUND tana aiwatar da ayyuka a matakin jiha da shiyya, don kowane yanki na ƙasar ya amfana da aiyukan hukumar, bana fannin da aka ba muhimmanci shine fannin ilimin likitanci”, in ji Masari.

Ya yi nuni da cewa asusun yana da tsarin bibiyar aiyukan da ake bayarwa, domin a tabbatar cewa makarantun suna kashe kuɗaɗen domin ayyukan da aka ware domin su.

Tsohon gwamnan kuma tsohon kakakin majalisar wakilai ta tarayya ya bayyana cewa a bana hukumar ta TETFUND ta samu mafi girman tallafin da ba ta taɓa samu, na Naira tiriliyan 1.6 wanda ya taru daga harajin ilimin da ake cirewa daga ribar da kamfanoni ke samu a ƙasar nan.

Ya ce ana cire kashi 3 cikin 100 daga ribar kowane kamfani, bisa yadda dokar da ta kafa hukumar TETFUND ta tanadar.

“A cikin wannan adadin, an ware kashi 40 cikin 100, wanda ya kai Naira miliyon dubu 460, domin gudanar da ayyuka daban-daban a manyan makarantun ƙasar nan.

“A matakin jiha an zaɓo manyan makarantu uku-uku; da jami’a ɗaya, da kwalejin kimiyya da fasaha ɗaya, da kuma kwalejin ilimi ɗaya, su ne zasu ci gajiyar shirin.

“Ayyukan sun dogara ne akan buƙatar da makarantun suka gabatar mana, suna rubuto mana buƙatunsu, mu kuma sai mu duba abin da ya fi muhimmanci da kuma kuɗaɗen da muke da su a ƙasa, sai mu amince musu mu sakar musu kuɗin”, in ji shugaban gudanarwan na TETFUND.

Masari ya bayyana cewa, daga cikin Naira Tiriliyan 1.65, an ware Naira niliyan 225 ga asusun bayar da lamunin ilimi ga ɗalibai (NELFUND), domin su fara ba ɗalibai rance a bana.

Ya ce an kuma ware Naira miliyan dubu 70 a matsayin tallafin inganta wutar lantarki a manyan makarantu, ya ce makarantun za su yi amfani da kuɗaɗen don haɗa na’urorin samar da wutar lantarki da hasken rana, wasu kuma da iskar gas.

Shugaban hukumar ta TETFUND ya kuma bayyana cewa hukumar ta samar da Naira miliyon 25,000 ga wasu manyan makarantu domin su samar da tsaro a makarantun.

“Makarantun za su yi amfani da kuɗaɗen ne domin inganta tsaro, wasu zasu sanya fitilun kan titi a harabobinsu da wasu aiyukan daban na samar da tsaro”, in ji Masari.

By ukarofi