NCAA ta dakatar da mawaƙi Kwam 1 daga hawa jirgi na tsawon wata shida

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Nijeriya (NCAA), ta ce za ta sanya Wasiu Ayinde, shahararren mawaƙin Fuji da aka fi sani da Kwam 1, a jerin waɗanda aka haramta wa hawa jirgi na tsawon watanni shida, saboda yadda halayyar da ya nuna a na Nnamdi Azikiwe, Abuja.

Daraktan hulɗa da jama’a da kariyar masu amfani na NCAA, Michael Achimugu, ne ya bayyana hakan a yayin wani taron manema labarai a jiya Alhamis.

“Abin da nake tabbatar wa jama’a shi ne, duk wanda ke da hannu a wannan al’amari za a hukunta shi,” inji Achimugu.

“A halin da muke ciki, an riga an yanke hukunci cewa ba zai samu damar hawa jiragen sama a Nijeriya ba har na tsawon watanni shida masu zuwa.

“Dokokin sufurin jiragen sama na kowa ne, domin kare lafiyar kowa. Waɗannan dokoki na duniya ne, ba don muzantawa ko cin zarafin wani ba aka samar da su.”

By ukarofi