Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano
Shugabar Asibitin Koyarwa na Jami’ar Northwest, wato Asibitin Nassarawa na Abdullahi Wase, Farfesa Hadiza Saidu Bala, kuma Shugabar ƙungiyar Iyaye da Malamai ta makarantar St. Louis da ke Kano, ta bayyana cewa, a matsayinta na tsohuwar ɗaliba sama da shekaru 35 da suka gabata, ta gamsu da yadda wannan makaranta ta shirya taron walimar yaye ɗalibai masu karatun Alƙur’ani mai girma a wannan makaranta mai tsohon tarihi wanda wannan walima ta ta zo karo na 20 akwai karfafa gwiwa da kyakyawar makoma ga ɗaliban wannan makaranta kuma mun gamsu da ƙokarin hukumar makarantar na bada ilimi da tarbiyya suke tafiya kafaɗa kafaɗa a wannan makaranta jiya da yau da aka samu cigaban na koyar da karatun Alƙur’ani mai girma a wannan makaranta ta St.Louis Kano inda kuma ta yabawa mataimakiyar shugabar makarantar ɓangaren gudanarwa Malam Halima Baba Yaro, inda ta buƙaci iyaye da sauran alumma su cigaba da haɗa kai domin samun yiwa yayanmu da jikokin mu kyakyawar tarbiyya domin amfanin duniyar mu da lahirar mu kamar dai yadda CMD Farfesa Hadiza Saidu Bala ta bayyana a wurin walimar saukar karatun Alƙur’ani mai girma karo na 20 da aka gabatar a ranar Lahadin nan.
Ita dai makarantar St. Louis wacce ta kai kimanin shekaru 69 da kafuwa a birnin Kano ɗalibai sama da 800 ne suka sauke Alƙur’ani mai girma a wannan makaranta ta St. Louis a Tsawan shekaru 20 da suka gabata kamar yadda aka bayyana a bikin sauka da akayi karo na 20 da fara ɓulo da koyar da karatun Alƙur’ani mai girma a wannan makaranta kamar dai yadda mataimakiyar shugabar makarantar Malama Halima Baba Yaro ta bayyana a bikin walimar saukar karatun ɗalibai 40 na wannan shekarar .
A ƙarshe Mataimakiyar Shugabar makarantar St.Louis Malama Halima Baba Yaro ta bayyana farin cikin ta kan yadda ake samun cigaba duk shekara a wannan ɓangare duk da karatun boko da ɗaliban suke yi tuƙuru a wannan makaranta amma bai hana wasu daga cikin ɗaliban da suka samu dama yin wannan karatu na Alƙur’ani mai girma ba kuma ta yabawa maaikatar ilimin jihar Kano da sauran masu ruwa da tsaki kan ilimi da hukumar makarantar kan wannan ƙokari da haɗin kai da ake samu ko da yaushe wajen gudanar da wannan karatu na Alƙur’ani mai girma a makarantar St. Louis Kano.
