Tallafi: Hadimin Gwamnan Kano ya gayyaci ’yan teburan Kantin Kwari

Spread the love

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano

Hon. Ibrahim Garba Kamfani, babban mai taimaka wa Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf kan harkar kasuwar Kantin Kwari ya gayyaci shugabanci ƙungiyar yan Tebura Mall da ke kasuwar kantin Kwari masu gwagwarmaya domin gwamnatin Kano ta tausaya musu na dawo musu da abubuwan da suka rasa na wuraren Sanaa wanda gwamnatin baya da ta gabata ta karɓe musu kamar yadda shi shugaban ƙungiyar yan Tebura Mall Alhaji Aminu Danfalke ya bayyana a wannan lokaci da suka amsa kiran SSA Alhaji Ibrahim Garba babban Mai taimakawa gwamna akan kasuwar Kantin Kwari Market Kano.

A jawabinsa Hon Ibrahim Garba Kamfani yace maƙasudin gayyatar shugabancin wannan ƙungiya ta ‘yan tebura na wannan kasuwa shi ne domin cigaba da tinawa gwamna Abba Halin da wannan mutane suke ciki kasancewar shi wannan gwamna mai jin tausayi da kukan mai ƙaramin karfi ne da kuma janwo na ƙasa yayi gaba wanda shi ne kowa ya san gwamna Abba Kabir da wannan hali don haka ne sukayi wannan taro inda aka tabbatar da tuni kan rubuce rubucen da yayi a matsayinsa na wanda gwamna ya wakilta wanda suke aiki tare da MD na Kantin Kwari Hon Saadu Dogon Nama da shugabancin ƙungiyar kasuwar kantin kwari na riko ƙarkashin shugabanci Abdullahi Sharu Na Malam, kuma suke ta ƙokarin tabbatar da manufar gwamnatin Kano wanda bata so ta ga an tauye hakin kowana mutum a jihar Kano kuma yasan da ikon Allah gwamna zai yi wani wajen warware matsalar nan dama sauran matsalolin alumma Kano.

Haka kuma ya ce akwai abubuwa da dama da suka taso na kuɗi ko wani abu mai kama da haka da ya cigaba da tunawa gwamna Abba da kansa ya zo ya warware matsalar a wannan kasuwa don haka wannan ma ba da dadewa ba in Allah ya so gwamnatin zata sha re wa yan tebura Mall hawayen su a wannan kasuwa da kuma kawo cigaba ta kowacce fuska da warware matsalolin wannan kasuwa da ma Kano baki ɗaya wanda shi ne burin gwamna Abba da jagora Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

A ƙarshe shi ma shugaban ƙungiyar yan Tebura Mall Alhaji Aminu Danfalke da ya samu rakiyar shugabanin yan ƙungiyar yabawa SSA kan wannan ƙokari na sa inda kuma yace babu wani mamaki na yin haka domin shi ne manufar gwamnatin Kano ta Alhaji Abba Kabir Yusuf na kyakyawar muamala da tausayawa na ƙasa da girmama na gaba kamar yadda ya kamata saɓanin wasu shugabanin da akasin haka suke rayuwarsu.

By ukarofi