NDC a shirye take ta haɗa kai da ADC, Atiku domin tunkarar zaɓen 2027 – Dickson

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Jagoran jam’iyyar NDC, sanata Seriake Dickson, ya bayyana cewa jam’iyyarsa a shirye take ta tattauna yiwuwar haɗaka da sauran jam’iyyun adawa musamman jam’iyyar ADC domin tunkarar babban zaɓen shekarar 2027.

Dickson, wanda ke wakiltar mazaɓar Bayelsa ta yamma a Majalisar Dattawa, ya bayyana hakan ne yayin wata hira da gidan talabijin na Channels Tɓ a shirin Sunday Politics.

Ya ce, duk da cewa NDC ta shafe kusan watanni biyar ne kacal da kafuwa, ta riga ta zama babbar jam’iyyar adawa a Nijeriya, kuma a shirye take ta shiga tattaunawa da sauran ‘yan adawa bayan kammala zaɓen fidda gwani.

Sai dai ya jaddada cewa duk wata haɗaka da za a yi bai kamata ta kawo sauyin ‘yan takarar da NDC ta riga ta tsayar ba.

“ƙofarmu za ta kasance a buɗe ga kowacce tattaunawar haɗaka. Amma muna fatan duk wata yarjejeniya za ta kasance bisa goyon bayan ‘yan takarar NDC, saboda mun yi imanin sun cancanta,” ya faɗa.

Dickson ya yi watsi da ra’ayin cewa NDC ba za ta iya fafatawa da shugaba Bola Tinubu da jam’iyyar APC ba.

A cewarsa, idan aka gudanar da zaɓe cikin gaskiya da adalci, APC za ta sha gagarumin kaye saboda ‘yan Nijeriya ba su gamsu da yadda ake tafiyar da mulki ba.

Ya kuma ƙalubalanci gwamnatin tarayya da ta bai wa dukkan jam’iyyun siyasa damar shiga zaɓen 2027 ba tare da wata tangarɗa ba.

“Idan kuna da tabbacin za ku yi nasara, ku bari duk jam’iyyar da ke son tsayawa takara ta shiga zaɓe. Nasara ta gaskiya ana samun ta ne daga akwatin zaɓe,” inji Dickson.

Da yake tsokaci kan hukuncin babbar kotun tarayya da ke Lokoja, wadda ta soke tsohon hukuncinta da ta yi na bai wa INEC umarnin yi wa NDC rajista, Dickson ya bayyana hukuncin a matsayin abin da bai da tushe kuma wani yunƙurin karkatar da hankali al’umma.

Ya ce kotun ba ta da ikon sake zama kan hukuncin da ta yanke a baya, yana mai cewa jam’iyyar ba ta amince da hujjojin da aka gabatar ba.

Dickson ya musanta rahotannin cewa an soke rajistar NDC, yana mai cewa babu wata hukuma da ta cire jam’iyyar daga rijistar INEC.

Ya bayyana cewa jam’iyyar ta gudanar da zaɓen fidda gwani na dukkan muƙaman siyasa cikin wa’adin da INEC ta tanada, kuma jami’an hukumar sun sa ido kan yadda tsarin ya gudana.

A cewarsa, abin da ya rage shi ne miƙa sunayen ‘yan takara ga INEC, kuma ba abin da zai rushe ingancin zaɓen fidda gwanin da jamiyyar ta y.

Dickson ya ce shi kansa ɗan takarar sanata ne a ƙarƙashin NDC, kuma ya tabbatar wa dukkan ‘yan takara da magoya bayan jam’iyyar cewa takarkarinsu suna nan daram.

Ya ƙara da cewa NDC za ta ci gaba da kare haƙƙinta ta hanyar bin doka tare da ci gaba da shirye-shiryen fuskantar zaɓen shekarar 2027.

By ukarofi

Leave a Reply