Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun ƙwayoyi ta ƙasa (NDLEA) ta ce ta kama mutum uku tare da hana jigilar ƙwayar hodar iblis da darajarta ta kai Naira biliyan 5.3 zuwa ƙasar Australia.
Mai magana da yawun hukumar, Femi Babafemi, ya bayyana cewa an gano ƙwayar ne a filin jirgin sama na Murtala Muhammed, inda aka kama kilo 17.9 na cocaine da aka ɓoye cikin zannuwa.
Babafemi ya ce an kama Olashupo Michael Oladimeji, wakilin jigilar kaya, sannan bincike ya kai ga cafke shugabannin ƙungiyar biyu — Muaezee Ademola Ogunbiyi da Shola Adegoke a Legas.
An kuma gano tabar wiwi da makami a gidajensu.
Ya ƙara da cewa shugaban ƙungiyar na ƙasashen waje, Adebisi Ademola Omoyele (“Mr. Bee”), na zaune a Dubai, yayin da wadanda aka kama suka taba yin zaman kurkuku a Birtaniya kan manyan laifuka.
A wani ɓangare, hukumar ta kuma kama wani ɗan Nijeriya, Gabriel Michael, a filin jirgin sama na Legas da ƙwayoyin tramadol 24,480 da yake shirin kaiwa Italiya.
Haka kuma, an gano robar codeine 160,200 a cikin mota mai ɗaukar kaya a tashar jiragen ruwa ta Onne, jihar Ribas, da kuma kama wani mai kai saƙonni a Abuja da kilo 3.1 na Colorado.
