
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Hukumar bada agaji ta gaggawa ta Ƙasa, NEMA ta raba kayan abinci ga mutanen da ibtila’in gobara a kasuwanni ya rutsa da su a Gusau na jihar Zamfara da jihar Sakkwato.
Shugaban NEMA reshen Sakkwato, Aliyu Shehu Kafindangi ya faɗi hakan a Gusau cikin wata sanarwa da ya fitar.
Ya ce tallafin kayan abinci na mutanen da lamarin ya afka mu su a farkon wannan shekarar ne wanda gwamnatin tarayya ta bayar domin a tallafa mu su.
Kafindangi ya ce, an yi rabon ne ta hanyar shirya tawaga ga kowane ɓangare don a tabbatar kowane ɗaya daga cikin waɗanda lamarin ya shafa sun samu kayan tallafin kamar yadda aka tsara.
Ya kuma ce, sun gudanar da hakan ne tare da samun haɗin gwiwa daga ma’aikatar jinƙai ta jihar Zamfara da kuma hukumar bada agaji ta gaggawa ta jihar Sakkwato.
