Nepal: Adadin mace-mace a zanga-zangar matasa ya ƙaru

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumomi a ƙasar Nepal sun ce adadin waɗanda suka rasu a yayin zanga-zangar Matasan a ƙasar Nepal da ke gudana ya kai 51 zuwa yanzu.

Kakakin ƴan sandan ƙasar, DIG Binod Ghimire ya bayyana haka a wata sanarwa, inda ya ce daga cikinsu akwai wata mata ƴar ƙasar Indiya, da wasu a yankin Kathmandu Valley da wasu gundumomi.

A wani ɓangare kuma, aƙalla fursunoni tara ne suka rasu yayin tashin-tashina a kurkuku, lamarin da ya yi sanadin tserewar kimanin fursunoni 13,000 a ƴan kwanakin nan duba da rashin tsarin kulawa da gidajen yarin ƙasar yadda ya dace.

A ranar Talata, Fraministan ƙasar KP Sharma Oli ya yi murabus daga kujerarsa bayan haramta amfani da kafafen sada zumunta ya janyo ƙone-ƙone, sace-sace da fito-na-fito da jami’an tsaro, lamarin da ya yi sanadin rasa rayuka da dukiyoyi da dama.

A ranar farko aka rasa mutane 21 daga cikin ƴan zanga-zangar, a cewar wani rahoton ƴan sandan ƙasar.

Ana sa ran ƴar siyasa Sushila Karki ta zama sabuwar framinista, lamarin da ka iya sa ta zama mace ta farko da ta samu muƙamin a ƙasar.

Shugaba Ram Chandra Paudel na shawartar jam’iyyun siyasar ƙasar, lauyoyi da ƙungiyoyin al’umma, inda da zarar an amince da buƙatar, za a naɗa ta nan ba da jimawa ba.

By Babaji