
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ƙungiyar Kansilolin Jam’iyyar APC (NPCF) ta karrama Gwamnan Jihar Kebbi, Dakta Nasir Idris da kyautar gwarzon gwamna na shekarar 2025.
NPCF ta ce, ta yi haka ne duba da yadda gwamnan ke ƙoƙarin farfaɗo da martaba da ci-gaban ƙananan hukumomin jiharsa.
A wata takarda da ta fitar da hannu Shugabanta, Hon. Muslihu Yusuf Ali, NPCF ta bayyana cewa a kwanan nan ne gwamnan ya ware Naira biliyan 2.85 domin biyan bashi da alawus ga kansiloli, ciyamomi da mataimakansu da sakatarori har ma da tsofaffinsu tun daga shekarar 1999 zuwa yanzu.
An ba gwamnan kyautar ne a lokacin da Hon. Muslihu Ali da ƴan tawagarsa suka kai wa gwamnan wata ziyara ta musamman a gidan gwamnatin jihar da ke Birnin Kebbi.
Da yake jawabi, Gwamna Idris, wanda ake wa laƙabi da Ƙauran Gwandu, ya yi godiya game da abinda ya kira ba-zata, yana mai fatan Allah ya ba shi ikon yi wa al’umma hidima sama da yadda yake yi a yanzu.
Haka ma Sakataren gwamnatin jihar, Hon. Yakubu Bala da Kwamishinan Harkokin Ƙananan Hukumomi, Hon. Abubakar Dutsen-Mari sun jinjina tare da yaba wa ƙungiyar akan ƙoƙarin wajen damuwa da matsalolin mambobinta.

