Gwamna Dikko Raɗda ya ce zai kashe kuɗi da yawa a aikin titin Sabuwa zuwa Tashar Bawa

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Aikin da zai ci kuɗi Naira biliyan 18.9bn yana da tsawon kilomita 27, sai dai dalilin ƙalubalen tsaro aikin ya tsaya.

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, ya bayyana cewa matsalolin tsaro da suka addabi ƙaramar hukumar sabuwa ne, babban dalilin da ya jinkirta fara aikin titin.

Aikin titin, wanda aka bayar da kwangilarsa kan kuɗi ₦18.9bn, an tsara shi ne domin haɗa Sabuwa da Tashar Bawa.

Ya ce aikin hanyar na ɗaya daga cikin alƙawarin yaƙin neman zaɓe ne da ya yi wa al’ummar Sabuwa.

Malam Dikko Raɗɗa ya fadi haka ne a lokacin da yake karɓar manyan jiga-jigai, ciki har da dattawa, hakimai, ‘yan kasuwa, ‘yan siyasa, malaman addini, wakilan matasa da sauran masu ruwa da tsaki daga ƙaramar hukumar Sabuwa, waɗanda suka kai masa ziyarar ban girma a fadan Gwamnatin Katsina.

Gwamnan ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta amince ta saki kuɗi har ₦7.5bn, wanda ke adadin kashi 40% na kudin fara aiki (mobilization), ga ɗan kwangilar aikin hanyar.

Gwamna Raɗɗa ya nuna ƙwarin gwiwa cewa da shirin sulhu da ke gudana a yankin, aikin titin da aka dade ana jira zai fara nan ba da daɗewa ba.

Ya lura cewa tattaunawa tsakanin al’ummomi da tubabbun ‘yan bindiga ya fara haifar da sakamako mai kyau, wanda ya samar da yanayin haɗin kai.

Gwamna Raɗɗa ya bayyana cewa da zarar an dawo da cikakken zaman lafiya, ɗan kwangilar zai sami ƙwarin gwiwar zuwa wurin aikin, don tabbatar da an gudanar da aikin titin cikin sauƙi kuma an kammala shi a lokacin da aka amince.

Dikko ya tabbatar wa mazauna yankin cewa gwamnatinsa ta ƙuduri aniyar ganin an kammala aikin kamar yadda aka alƙawarta.

Da yake sake nanata ƙa’idojin da ke jagorantar manhajar “Gina Makomarku” (Building Your Future), gwamnan ya bayyana cewa ci gaban da gwamnatinsa ke samu a sassa daban-daban yana faruwa ne saboda bin tsarin manufofi masu kyau.

Ya bayyana da alfahari cewa gwamnatinsa ta riga ta cika kusan kashi 90% na alƙawuran yaƙin neman zaɓen sa, yana mai bayyana hakan a matsayin wani yunkuri na gangan don gyara mummunan ra’ayin da ake yi wa ‘yan siyasa cewa sukan kasa cika alƙawuransu.

Gwamna Raɗɗa ya ƙara da cewa rashin tsari mai kyau ya hana samun ci gaba mai ma’ana tsawon shekaru, yana mai danganta gazawar shugabannin baya da rashin tsarin manufofi mai kyau.

Ya kuma tabbatar wa tawagar cewa gwamnatinsa ta ƙuduri aniyar inganta rayuwar al’ummar jihar baki ɗaya.

Gwamnan sai yayi kira ga al’ummar Sabuwa da su kasance masu haɗin kai, da ba gwamnatin sa goyon baya a yunƙurin da take masu kawo ci gaba cikin gaggawa.

Da yake jawabi a madadin tawagar, Injiniya Tasiu Abubakar, wani dattijo kuma fitaccen ɗan jam’iyyar APC a yankin, ya ce tawagar ta haɗa da dukkan masu ruwa da tsaki — manyan ‘yan kasuwa, jami’an jam’iyya, sarakunan gargajiya, malaman addinin Musulunci, da wakilan matasa.

Ya gode wa Gwamna Radda don bayar da muhimman ayyuka ga Sabuwa da kuma naɗa ‘yan asalin yankin a gwamnatinsa. Ya kuma yabawa gwamnan musamman don amincewa da aikin titin kilomita 27 wanda zai hada Sabuwa da Tashar Bawa.

Injiniya Abubakar ya kuma roki gwamnatin jihar da ta sa baki kan aikin Gwamnatin Tarayya na Cibiyar Noma (Agricultural Park Project) da aka watsar a Sabuwa, wanda aka fara a lokacin mulkin tsohon Shugaban ƙasa Goodluck Jonathan.

Ya jaddada muhimmancin farfaɗo da aikin, yana mai nuna cewa cibiyar guda biyu ne kawai aka amince da su a duk faɗin ƙasar,ɗaya a Katsina, daya kuma a Jihar Ondo.

Ya jaddada cewa farfaɗo da aikin ba kawai zai maido da ƙwarin gwiwa ga al’umma ba ne, har ma zai mayar da Sabuwa cibiyar noma,da zai samar da ayyukan yi , da kuma inganta samar da abinci a yankin.

A nasa jawabin, Hon. Danjuma Ibrahim, dan majalisa mai wakiltar yankin Sabuwa a Majalisar Dokokin Jihar , ya bayyana cewa tubabbun ‘yan bindiga a yankin sun nuna shiri don shiga yarjejeniyar sulhu da mazauna yankin.

Ya bayyana cewa wannan ci gaba wani babban mataki ne zuwa ga dawo da zaman lafiya da tsaro a Sabuwa, yayin da yake nuna cewa da yawa daga cikin wadanda suka taba taimakawa wajen rashin zaman lafiya yanzu sun amince su ajiye makamansu kuma su koma cikin al’umma.

A cewarsa, ma’aikatar tsaro ta cikin gida (Ministry for Internal Security) an riga an sanar da ita kuma tana aiki don tabbatar da cewa an shirya tsarin da kyau, mai gaskiya, kuma mai dorewa, da nufin tabbatar da kare rayuka da dukiyoyi yayin samar da yanayi mai ɗorewa don ayyukan ci gaba.

By ukarofi