An zargi tsohon alƙalin wasa Coote da cin zarafin yaro

Spread the love

An tuhumi tsohon alkalin wasan Firimiya David Coote da fitar da hoton da ya zama cin zarafin yaro.

Tsohon jami’in, mai shekaru 43 kuma daga Collingham, zai gurfana a gaban Kotun Majistare ta Nottingham ranar Alhamis.

Laifin ya shafi rabawa ko adana hotuna ko bidiyo cin zarafin da ya shafi faifan bidiyo da jami’an ‘yan sandan Nottinghamshire suka kwaso a watan Fabrairu, inji rundunar.

An gurfanar da Coote a ranar 12 ga watan Agusta kuma yana kan beli.

Mahukutan kwamitin rafli sun kori Coote a watan Disamba, bayan wani faifan bidiyo na kalaman ɓatanci da ya yi kan tsohon kocin Liverpool Jurgen Klopp a shekarar 2020 da ya fito fili.

Hukumar ƙwallon ƙafar Turai UEFA ta dakatar da shi har zuwa ranar 30 ga watan Yuni 2026 bayan wani faifan bidiyo daban da ya fito na nuna shi yana shekar foda, yayin da yake Jamus don gasar Euro 2024.

A cikin Janairu Coote ya fito ya bayyana kansa a matsayin ɗan luwaɗi, kuma ya ce gwagwarmayar rayuwa ya sa ya ɓoye, hakan ya bayar da gudummawa da ɓacin rai game da Klopp da kuma amfani da muggan ƙwayoyi.

A watan Agustan bana kuma hukumar ƙwallon ƙafa ta Ingila ta dakatar da shi na tsawon makonni takwas saboda faifan da ya yi kan Klopp. Mai magana da yawun Coote ya ƙi cewa komai lokacin da aka tuntuɓe shi.

By ukarofi