Netherlands ta amince da mayar da abin tarihin Fir’auna da aka sace ga Masar

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Gwamnatin Netherlands ta sanar da cewa za ta miƙa wani abin tarihi mai shekara 3,500 da aka sace a lokacin tashin hankalin Arab Spring ga Masar, a wani mataki da masana suka ce na tabbatar da mutunta kayan tarihi da martabar al’adu.

Rahotanni sun ce wannan sassaƙaƙƙen akwatin ajiye mutum daga zamanin sarautar Fir’auna Thutmose na Uku an yi amannar an fitar da shi ba bisa ƙa’ida ba a shekarar 2011 ko 2012. Sai dai shekaru bayan nan, aka sake gano shi a bikin nune-nunen fasaha a birnin Maastricht, bayan wata bayanai da aka bai wa hukumomin ƙasar da suka gano asalin sa.

Firayim Ministan Netherlands mai barin gado, Dick Schoof, wanda ya halarci buɗe sabon gidan ajiye kayan tarihi na Grand Egyptian Museum a Giza, ya tabbatar da cewa ƙasar sa za ta miƙa sassan ga Masar nan da karshen wannan shekarar. Kakakin gwamnati ya bayyana kayan tarihin a matsayin muhimmin ginshiƙi ga tarihin Masar da al’adanta.

An bayyana cewa dillalin da ya kawo kayan nune-nunen ya miƙa shi da kansa bayan hukumomi sun tabbatar da cewa an samo shi ta hanyar da ba ta dace ba.

Masar ta ƙaddamar da gagarumin gidan tarihin Grand Egyptian Museum, wanda ya ɗauki sama da shekaru uku ana ginawa, tare da kayayyakin tarihi fiye da 100,000 ciki har da kayan kabarin Sarki Tutankhamun da mashahurin akwatinsa na zinariya. Masana sun ce wannan babbar cibiyar tarihi za ta kara wa Masar ƙarfin kai wajen neman a dawo mata da sauran manyan kayayyakin tarihi da ke kasashen waje, ciki har da sanannen Rosetta Stone da ke a Birtaniya.

ƙasar Masar na sa ran karɓar wannan sabon akwatin abin tarihi kafin ƙarshen shekarar.

By ukarofi