Daga RABIU SANUSI a Kano
Gwamnatin Jihar Kano ta tabbatar da ƙudurinta na ci gaba da tallafawa da kuma sake tsare tarbiyya ga matasa tubabbun ‘yan daba, ta ƙarƙashin shirin Safe Corridor, wani shiri na musamman da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ƙirƙiro domin dakile ta’addanci da tashin hankali a tsakanin matasa tare da tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa a faɗin jihar.
Wannan tabbacin ya tabbata ne a lokacin da Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida, Kwamared Ibrahim Waiya wanda kuma shi ne Kwamandan Shirin Safe Corridor na Jihar Kano, ya jagoranci taron hadin gwiwa tsakanin jagorancin matasa tubabbun yan daba daga ƙananan hukumomin birni guda takwas da kuma Kwamitin Tsakiya na shirin.
Taron ya samu halartar fitattun dattawan al’umma da shugabanni masu ruwa da tsaki a cikin shirin, kamar su Alhaji Mohammed Shehu (Sarkin Shanu), Alhaji Gidado Muktar, Alhaji Aliyu Harazimi Umar (ɗan Amar), da wasu.
A jawabinsa, Kwamishinan ya bayyana shirin a matsayin daya daga cikin ayyukan da suka fi taba zuciyarsa a rayuwar aikinsa na hidimar jama’a. Ya ce zuwa yanzu, an riga an tantance matasa 1,600 da suka ayyana tuba, kuma ana ci gaba da basu horo na farkon mataki.
Daga nan kuma kowannensu zai shiga matakin sake gyara dabi’a bisa ga sakamakon tantance buƙatarsa da ake yi tare da Hukumar NDLEA.
Har ila yau, gwamnati na shirin tantance karin matasa 2,100 da su ma suka nuna aniyarsu ta barin ɗabi’ar tada hankali tare da rungumar zaman lafiya da halin kirki.
“Baya ga wannan adadi, akwai labarin rayuwa da gaske,” inji shi. “Waɗannan matasa sun fuskanci mawuyacin hali a baya, amma a yau sun zaɓi su dawo su gyara kansu, su zama masu amfani ga kansu da kuma al’umma baki ɗaya.
Kwamishinan ya ce rawar da gwamnati ta ɗauka ita ce ta jagoranci da ba da shawarwari, horo, tallafi, sake koyar da su sana’o’i, da kuma gina basira wacce za ta dawo da su cikin al’umma ta gari.
“Lokacin da muka saka hannun jari wajen gyara matasa tubabbun yan daba, ba wai muna canza rayuwar mutum guda ba ne, muna inganta tsaro da ɗorewar zaman lafiya a cikin al’umma gaba ɗaya.
Ya ƙara da cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sanya wannan shiri a matsayin ginshiƙin aniyar samar da zaman lafiya da ci gaba mai ɗorewa a Kano.
Kwamishinan ya kuma tabbatar da cewa duk alƙawuran da aka yi wa matasan za a cika su ba tare da wani jinkiri ba.
Ya yi kira ga matasan da su ci gaba da jajircewa a wannan sabon tafarki na rayuwa mai kyau, tare da kiyaye ladabi da tarbiyya.
“Ga matasarmu tubabbun yan daba, ina muku jawabi cikin gaskiya: ku tsaya a kan wannan hanya.
“Ku zama abin koyi ga wasu. Ba wai kawai za a gyara ku ba ne, za a sake fito da ku cikin sabon kamanni, a matsayin jakadu na zaman lafiya da cigaba,” inji shi.
A ƙarshe, ya bayyana shirin Safe Corridor a matsayin shaida mai ƙarfi da ke nuna cewa gyara da dawo da mutum tuba na yiwuwa idan al’umma ta zaɓi tausayi maimakon tozarci.
