Nijeriya @66: NLC ta buƙaci rage farashin fetur da kawo sabon albashi

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Kungiyar ƙwadago ta Nijeriya (NLC) ta buƙaci Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta gaggauta rage farashin man fetur, ta amince da biyan ma’aikata ƙarin tallafin kuɗin albashi na ƙasa baki ɗaya, tare da fara tattaunawa kan sabon mafi ƙarancin albashi, yayin da ta bayyana cewa al’ummar Nijeriya na fuskantar wani yanayi na tsananin matsalar rayuwa.

NLC ta bayyana hakan ne a cikin saƙon ranar samun ’yancin kai da shugaban ƙungiyar, Joe Ajaero, ya sanya wa hannu a ranar Laraba, 30 ga Satumba, 2026. ƙungiyar ta ce hauhawar farashi ta rage darajar albashin ma’aikata, yayin da tashin farashin man fetur da sufuri ya ƙara tsadar abinci, kuɗin makaranta, haya da sauran abubuwan buƙatun yau da kullum.

A cewar NLC, “mun tsaya ne a bakin ƙofar wata babbar matsalar tsira”, inda ta ce hauhawar farashin kayayyaki ta ci ƙarfin albashin ma’aikata. Ta ƙara da cewa man fetur na sayarwa kusan Naira 1,430 ko fiye kan lita a manyan birane, yayin da farashin ya fi haka a wasu yankunan da ke da nisa.

Kungiyar ta ce ƙarin farashin man fetur da aka samu a watan Mayun 2023 bayan cire tallafin mai ya kasance abin da ta kira “farmaki kai tsaye kan ma’aikata”, tare da tambayar inda aka karkatar da kuɗaɗen da gwamnati ta ce za ta samu bayan cire tallafin.

NLC ta ce gwamnati ta bayyana cewa cire tallafin man fetur zai samar da kuɗaɗen da za a zuba wajen gina ababen more rayuwa da inganta ayyukan jin daɗin jama’a, amma shekaru uku bayan haka, farashin man fetur ya ninka sau da dama, yayin da take cewa alkawurran da aka yi na samar da ababen more rayuwa da ayyukan jin daɗin jama’a ba su kai ga matakin da ake tsammani ba.

“Gwamnati ta ce cire tallafin mai zai ’yantar da kuɗaɗe domin ababen more rayuwa da ayyukan jin daɗin jama’a. Bayan shekaru uku, farashin man fetur ya ninka sau da dama, amma ababen more rayuwa da ayyukan jin daɗin jama’a da aka yi alkawari har yanzu ba su bayyana yadda ya kamata ba. Ina aka kai kuɗaɗen da aka samu daga cire tallafin? ’Yan Nijeriya sun cancanci samun amsa, kuma suna buƙatar ta yanzu,” inji ƙungiyar.

NLC ta kuma soki dogaro da Nijeriya ke yi kan man fetur da ake tacewa a ƙasashen waje, duk da cewa ƙasar ita ce mafi girman mai samar da ɗanyen mai a Afirka. A cewarta, hakan ya sanya ma’aikata cikin haɗarin sauyin farashin man fetur da ke faruwa a kasuwannin duniya.

ƙungiyar ta ce buƙatarta ta farko ita ce gwamnati ta nemi hanyoyin da za ta rage farashin man fetur nan take, saboda tsadar sufuri na daga cikin manyan hanyoyin da hauhawar farashi ke shafar rayuwar ’yan Nijeriya.

“Ba tare da yanke wannan silsilar ba, duk wani ƙoƙari na rage wahalhalun jama’a ba zai yi tasiri ba,” inji NLC.

ƙungiyar ta kuma buƙaci a gaggauta aiwatar da wani sabon tsarin ƙarin kuɗin albashi ga ma’aikata a matakin tarayya, jihohi da ƙananan hukumomi.

“Albashi ba sadaka ba ne. Mataki ne na gaggawa domin daƙile durƙushewar ainihin darajar kuɗin shiga,” inji NLC.

Haka kuma, ƙungiyar ta buƙaci gwamnati ta aiwatar da rangwamen harajin da aka amince da shi a tattaunawar da aka yi tsakanin gwamnati da ƙungiyoyin ƙwadago a watan Oktoban 2023. Ta ce rangwamen harajin da aka tanada a cikin yarjejeniyar fahimtar juna da ɓangarorin biyu suka sanya wa hannu har yanzu ba a aiwatar da shi ba.

Dangane da batun albashi kuwa, NLC ta buƙaci a gaggauta kafa kwamitin haɗin gwiwa da ya ƙunshi gwamnati da ma’aikata da masu ɗaukar ma’aikata, domin tsara da kuma samar da sabon tsarin mafi ƙarancin albashi na shekarar 2027 kafin ƙarshen wannan shekara.

ƙungiyar ta ce mafi ƙarancin albashin Naira 70,000 da ake amfani da shi yanzu ya riga ya rasa ƙima saboda hauhawar farashi tun kafin ma aiwatar da shi.

NLC ta kuma buƙaci a rage kuɗaɗen gudanar da gwamnati tare da ƙara nuna gaskiya, tana mai cewa gwamnati ya kamata ta fara da kanta wajen rage almubazzaranci a lokacin da ake buƙatar ma’aikata su ƙara ɗaure ɗamara.

Baya ga buƙatunta na gaggawa, ƙungiyar ta nemi ƙara saka hannun jari wajen hanyoyi da sauran ababen more rayuwa, tare da inganta asibitoci, makarantu da sauran ayyukan jin daɗin jama’a.

Ta kuma buƙaci samar da damarmaki ga matasa, tana mai cewa ya kamata matasa su ga fata da damar samun makoma mai kyau, maimakon a riƙa yi musu magana kawai kan fata.

Dangane da matsalar tsaro kuwa, NLC ta ce tashe-tashen hankula sun ƙara dagula yanayin tattalin arziki tare da barazana ga zaman lafiyar ƙasa. Ta ce kusan ’yan Nijeriya 2,000 ne suka rasa rayukansu sakamakon tashin hankali a cikin watanni ukun farko na shekarar 2026, lamarin da ta ce ya sanya manoma, malamai da likitoci kasa gudanar da ayyukansu a wasu yankuna.

ƙungiyar ta danganta talauci, rashin aikin yi, rashin fata da kuma rashin daidaito da matsalar tashin hankali da aikata laifuka, tana mai cewa ba za a iya magance matsalar tsaro ba tare da magance matsalolin rabon arziki da adalci a cikin al’umma ba, sannan ba za a samu farfaɗowar tattalin arziki mai ɗorewa ba tare da magance matsalar tsaro ba.

Yayin da ake tunkarar babban zaɓen shekarar 2027, NLC ta gargadi ’yan siyasa da kada su yi amfani da zaɓe wajen magudin sakamako, tsoratar da masu kaɗa ƙuri’a ko kuma amfani da kalaman da za su rura wutar rikicin ƙabilanci da addini.

ƙungiyar ta ce idan lokaci ya yi, za ta yi amfani da kundin Workers’ Charter domin bayyana manufofi da ’yan takarar da take ganin sun cancanci samun goyon bayan ma’aikata.

Sai dai ta jaddada cewa ma’aikata suna da ’yancin yin tunani, yanke hukunci da kuma zaɓin siyasa da kansu.

“ƙungiyar Ma’aikata ta Nijeriya za ta ci gaba da tsayawa a kan buƙatun ma’aikata, tana gwagwarmaya har ƙarshe domin samar da albashi mai daraja, wuraren aiki masu aminci da kuma rayuwar da ke cike da mutunci,” inji Ajaero.

By ukarofi

Leave a Reply