Nijeriya da Saudiyya sun ƙulla yarjejeniyar tsaro domin ƙarfafa haɗin gwiwar soja

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Nijeriya da Saudiyya sun rattaɓa hannu kan muhimmin yarjejeniya a ranar Talata domin zurfafa haɗin gwiwar tsaro da soja tsakanin ƙasashen biyu.

Wannan mataki na zuwa ne a lokacin da Nijeriya ke fama da ƙalubalen tsaro iri-iri, tana kuma neman ƙarin goyon bayan ƙasashen duniya don farfaɗo da ƙarfinta na soja. Ministan ƙaramin Harkokin Tsaro na Nijeriya, Bello Matawalle, da Mataimakin Ministan Tsaron Saudiyya mai kula da Harkokin Gudanarwa, Dr Khaled Al-Biyari, su ne suka sanya hannu kan yarjejeniyar a Abuja.

A cewar sanarwar da Blueprint Manhaja ta gani, wacce Jami’ar Hulɗa da Jama’a ta Ma’aikatar Tsaro, Enderline Chukwu, ta fitar, an ce yarjejeniyar na da nufin inganta tsarin tsaro na Nijeriya tare da faɗaɗa ƙwarewar rundunonin sojinta.

Matawalle ya bayyana yarjejeniyar a matsayin “babban ci gaba,” wacce za ta ba da damar haɗin gwiwa a fannonin horo, atisayen soji na haɗin gwiwa, musayar bayanan sirri, tallafin fasaha, kayan aiki da sauran shirye-shiryen tsaro da ƙasashen biyu suka amince da su.

Yarjejeniyar za ta fara aiki na tsawon shekaru biyar, tare da yiwuwar sabuntawa. Kowace ƙasa na da damar janye kanta daga yarjejeniyar da sanarwar diflomasiyya ta watanni uku.

Ya ce ana sa ran wannan haɗin gwiwa zai haifar wa Nijeriya da ƙarin fa’ida, musamman wajen yaƙi da ta’addanci, ƙara inganta horon manyan jami’an soja da kuma ƙarfafa shirin soji ta hanyar atisayen haɗin gwiwa.

Nijeriya da Saudiyya na da dogon tarihin hulɗar diflomasiyya, al’adu da tattalin arziki, musamman saboda alakar addini ta hanyar aikin Hajji da Umrah. Haka kuma, ƙasashen biyu na aiki tare a cikin ƙungiyoyin duniya kamar OIC.

A ‘yan shekarun nan, dangantakar ta zurfafa zuwa batutuwan zuba jari, makamashi da yanzu harkar tsaro, wanda ke nuna sabuwar tsayin daka wajen faɗaɗa dangantakar dabarun tsaro tsakanin Abuja da Riyadh.

Nijeriya na fuskantar rikice-rikice mabambanta a sassa daban-daban na ƙasa. A Arewa maso Gabas, har yanzu Boko Haram da ISWAP na kai hare-hare. Fashin daji da garkuwa da mutane sun yi kamari a Arewa maso Yamma, yayin da rikice-rikicen manoma da makiyaya ke ci gaba a Arewa ta Tsakiya.

A Kudu maso Gabas kuwa akwai matsalar ƙungiyoyin ‘yan separatist, sannan a Kudu maso Kudu satar albarkatun mai da laifukan teku na ci gaba.

Waɗannan matsalolin sun kawo gagarumin nauyi kan rundunonin tsaro na Nijeriya, abin da ya sa haɗin gwiwar tsaro na ƙasashen duniya, kamar wannan yarjejeniya da Saudiyya ya zama muhimmin mataki na ƙarfafa ƙarfin tsaron ƙasa.

By ukarofi