Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
‘Yan Chana da ‘yan Philliphine kusan 200 ne kotu a tarayyar Nujeriya ta kama bisa laifin damfara ta yana ta gizo.
Hukumar Kula da Shige da Fice ta ƙasa (NIS), wadda ta bayyana hakan, ta ce za a fara aikin ne a ranar Lahadi 18 ga watan Agusta, 2025.
Waɗanda aka kora, waɗanda su ne kashi na farko cikin mutane 192 da aka yanke wa hukuncin, an shirya za su bar Nijeriya ne a ranar Lahadi da yamma.
Suna daga cikin mutane 759 da aka kama yayin wani gagarumin samame da aka kai a ranar 10 ga Disamba, 2024, a Oyin Jolayemi Street, Victoria Island, Legas.
A cewar NIS, za a kwashe ƙarin wasu rukunin mutanen da aka kora a ranakun Litinin da Talata, inda za a kammala aikin mayar da su ƙasashen su.
Tuni dai aka mayar da dukkan waɗanda aka yankewa hukuncin zuwa Hukumar Kula da Shige da Fice domin a kai su ƙasashensu na asali.
ƙungiyar ta kasance tana gudanar da babban zamba ta yanar gizo da kuma shirin Ponzi kafin a tattara ta a wani aikin haɗin gwiwa.
A cewar Hukumar da ke Yaƙi da Masu Yi Wa Tattalin Arzikin ƙasa Zagon ƙasa (EFCC) da ta gurfanar da waɗanda ake zargin, an yankewa wasu baƙi 192 ’yan ƙasashen waje da suka haɗa da ‘yan Chana da Philippine hukuncin ɗauri kan badaƙalar.
Da yawa daga cikin tuhume-tuhumen sun haɗa da zargin yin amfani da bayanan ƙarya ta yanar gizo don damfarar waɗanda abin ya shafa, horar da ma’aikatan kamfanin Genting International Co. Limited kan ayyukan damfara, da sauran laifuka ƙarƙashin dokar cin hanci da rashawa da sauran laifuka masu alaƙa ta 2006.
Hukumar ta EFCC ta bayyana cewa tuhumar ta bayyana manyan laifuka da ke da nufin zagon kasa ga tsaron Nijeriya da kuma harkokin kuɗi ta hanyar aikata laifuka ta yanar gizo da kuma ayyukan damfara.
Shugaban Hukumar EFCC, Ola Olukoyede, ya bayyana hukuncin da korar da aka yi masa a matsayin wani ci gaba a yakin da Nijeriya ke yi da aikata laifuka ta yanar gizo da zamba.
Ya nanata ƙudurin hukumar na ƙara tsananta bincike, kwato kuɗaɗen da aka wawashe, da kuma dawo da martabar kasa bisa tsarin yaƙi da cin hanci da rashawa na Shugaba Bola Tinubu.
Harin na watan Disamba, wanda ake yi la’akari da shi a matsayin ɗaya daga cikin mafi girman ayyukan yaƙi da ta’addanci a Nijeriya, ya kawo sauyi a yaƙi da laifuffukan kudi na ƙasa da ƙasa.
Baƙin dai na zama masu ƙirƙirar makarantun koyar da fasahar damfara da ke ta ɓulla a cikin tarayyar Nijeriyar a halin yanzu.
Duk da cewar suna shiga ƙasar da sunan zuba jari a fannonni daban-daban na ci gaban al’umma, ana kallon ƙaruwar rawa ta bakin na waje a cikin masana’anta ta damfara da ke bunƙasa a cikin tarayyar Nijeriyar a halin yanzu.
Kuma ko a baya bayan nan mahukuntan Nijeriyar sun tasa keyar wasu Sinawa 42 zuwa wajen ƙasar bayan samunsu da laifin damfara ta yana ta gizo.
Aƙalla wasu baƙi kusan 200 da mafi yawansu yan Chinan wata kotu a Nijeriyar ta yanke wa hukunci bayan kama su cikin wata makarantar koyar da dabarun damfara.
Karkatar da kai zuwa ƙasar Chana a ɓangaren mahukuntan Nijeriyar cikin neman jarin waje ne daga dukkan alamu ke tasirin wajen kwararar masu laifin daga Chana.
ƙasar Chana ce dai ke zaman ta kan gaba a halin yanzu a ƙoƙarin sake ginin hanyoyi da tashoshin jiragen sama da na ruwa ko bayan haƙar ma’adinai iri-iri a tarayyar Nijeriyar.
To, sai dai kuma a cikin neman jarin na waje Nijeriyar ta ke kallon ƙaruwar aikata laifukan yanar gizo, dama ragowar da ke da ruwa da tsaki da ƙoƙarin arzikin dare ɗaya.
Koma ya take shirin kayawa tsakanin zuba jari da taka rawa a laifuka iri-iri, daga dukkan alamu rawa ta baƙin na waje na tasiri bisa suna da kila ma tasirin ƙasar a idanun duniya a halin yanzu.
Ya zuwa yanzun dai ’yan Nijeriya da ma makwabciyar su Ghana na ji har a tsakar kai a ƙoƙarin wankin suna walau cikin neman izinin zirga-zirga a duniya ko kuma kasuwar da ke da babban tasiri a rayuwa da makoma.
