Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano
Jagora kuma fitacce daga cikin sharifan Ahalil baitin Nijeriya, Alhaji Sharif Haruna Abba Garin Ali, ya ce babu wata ɗaukaka a duniya ta fi a ce kai sharifi ne jikan Manzon Allah (SAW), don haka duk wata sarauta ka sameta. Ya ce wannan ce ta sa bai yadda ya zama Sarkin Sharifai ba domin lokacin da Sarkin Sharifan Nijeriya Alhaji Abba Fari ya yi wafati a Dutsinma shi aka fara yi wa tayin kujerar “domin ba zan iya sabo ni kullum bana son ya zama kamar ina neman wata ɗaukaka ko neman abun duniya ne da wannan sarauta domin harkar kasuwanci da ayyukan kamfanina na gode wa Ubangiji ba sai na nemi wani abu ba da sunan sharifta ba, kamar dai yadda wasu sharifan ke neman abun duniya ta wannan hanya maimakon kasuwanci ko sana’a da za ta kare motuncinsu da ƙara daraja a wajen Allah da al’umma bakiɗaya,” inji shi.
Haka kuma daga ne yada masulke ke tafiyar ƙasar nan abun taka ce ta yadda suka manta da bunƙasa ilimi, lafiya, noma, hanyoyi da dai sauransu a yankunan karkara musamman ta yadda ya bada misali da yadda ƙauyukan Jigawa suka fi na Kano cigaba ta hanyoyi, ruwan sha, da hasken wutar lantarki mafi yawanci jihohin ƙasar nan sun fi Kano samun wutar lantarki kuma aikin samar da tashar lantarkin Kano a 2012 zamanin Gwamna Kwankwaso ta kwana? duk ta kai kashi 70 cikin 100 gashe ana ƙarshen 2025 jama’ar Kano na buƙatar wutar tunda ita ce cibiyar kasuwanci Arewa.
A ƙarshe Ahalul baiti Garin Ali ya ce akwai buƙatar mutane dattawa masu mutunci su shiga siyasa don gyara tsarin zaɓe da shugabancin ƙasar nan daga hannun gurɓatattun ‘yan siyasa masu gurɓata tarbiyyar matasa, wanda duk ba su san muhimmancin zaɓen nagari ba.
