Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Kasuwar hannun jari ta Nijeriya ta fuskanci mummunar durƙushewa a makon farko na watan Nuwamba, inda aka yi asarar kimanin Naira Tiriliyan 2.8 sakamakon tashin hankali a siyasar duniya da ya dagula hankalin masu zuba jari.
Rahoton News Point Nigeria ya bayyana cewa wannan koma baya ya biyo bayan barazanar Shugaban Amurka, Donald Trump, wanda ya yi gargaɗi kan yiwuwar tura dakarun soji zuwa Nijeriya saboda zargin rashin kulawar gwamnati kan cin zarafin addini.
A makon da ya gabata, Trump ya ayyana Nijeriya a matsayin “ƙasar da Za A Sakawa Ido” (Country of Particular Concern) — yana mai cewa gwamnatin Amurka za ta katse duk wani tallafi ga Nijeriya tare da yiwuwar ɗaukar matakin soja, muddin ba a daƙile kisan Kiristoci da ake zargi ba.
Wannan jawabi mai zafi ya haifar da rudani a cikin kasuwannin kuɗi na duniya, inda masu zuba jari — na gida da na waje — suka fara sake duba haɗarin da ke tattare da saka hannun jari a Nijeriya.
A cewar Nigerian Exchange Limited (NGX), an samu asara a dukkan zaman ciniki guda biyar daga Litinin 3 zuwa Juma’a 7 ga Nuwamba.
A ranar Litinin, rana ta farko bayan barazanar Trump, darajar kasuwar hannun jari ta faɗi daga naira tiriliyan 97.829 zuwa tiriliyan 97.582, wanda ke nuna asarar naira biliyan 244.9 a rana guda.
All-Share Indeɗ (ASI) na NGX ya ragu da kashi 0.25%, inda ya sauka zuwa makin 153,739.11, lamarin da ya sauke ribar da masu saka hannun jari ke da ita zuwa +49.37% a shekarar.
ɓangarorin banki, mai da iskar gas, masana’antu da kayan masarufi sun fi fuskantar asara, inda duk ribar da aka samu a watan Oktoba ta ɓace sakamakon fitar da jarin masu saka hannun jari.
Masana harkar zuba jari sun bayyana cewa wannan martani mai tsanani yana nuna yadda rashin tabbas a siyasa ke iya rugujewa cikin gaggawa.
“Maganganun Shugaba Trump sun ƙƙra tayar da hankalin masu zuba jari a duniya,” inji wani mai dabarar saka hannun jari da ke Legas.
“Jarin waje ya fara ja da baya, yayin da na cikin gida suka nuna damuwa sosai.”
