Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Rundunar Sojojin Ruwa ta NIjeriya ta sake yin abin yabo, bayan da ta ceto ma’aikatan jirgin ruwa goma da suka tsinci kansu cikin hatsari a lokacin da jirginsu, MV SEMA III, ke nitsewa a tsakiyar tekun Kalaba.
A cewar sanarwar da Daraktan Hulɗa da Jama’a na Rundunar, Commodore A. Adams-Aliu, ya fitar, jami’an rundunar daga sansanin Forward Operating Base (FOB) Ibaka ne suka samu kiran gaggawa daga jirgin da ke kan hanyarsa daga Malabo, Eƙuatorial Guinea, zuwa Kalaba.
An bayyana cewa Sojojin Ruwa sun karɓi kiran ne da misalin ƙarfe 8 na dare, inda nan da nan suka tura kwale-kwalen yaƙi da ke ɗauke da na’urar tsotse ruwa zuwa wurin.
“Da isar jami’an, sai suka tarar da jirgin yana shan ruwa sosai. Nan take suka ceto dukkan mutane goma da ke cikin jirgin — mutum ɗaya ɗan ƙasar Kamaru, ɗaya ɗan Eƙuatorial Guinea, da kuma ’yan Nujeriya takwas,” inji sanarwar.
An kai mutanen sansanin FOB Ibaka inda aka kula da lafiyarsu, aka tambaye su, sannan aka basu jinya kafin a sake su washegari, Asabar 8 ga Nuwamba, 2025.
Kyaftin ɗin jirgin MV SEMA III ya bayyana godiya ga Sojojin Ruwa bisa yadda suka nuna ƙwarewa da gaggawa, yana mai cewa “da taimakonsu ne tsakanin rai da mutuwa a teku.”
Wannan aikin ceto, kamar yadda rundunar ta bayyana, ya nuna yadda Rundunar Sojojin Ruwa ke ƙara ƙwarewa da himma a ƙarƙashin jagorancin Shugaban Sojojin Ruwa (CNS), Vice Admiral Idi Abbas.
A cikin watanni baya-bayan nan, rundunar ta ƙara kaimi wajen yaƙi da matsalolin tsaro a ruwa, satar mai, fashin teku, da kuma hana satar albarkatun kasa — matakan da suka ƙara tabbatar da tsaro da amincewa a harkokin ruwa da tattalin arzikin “Blue Economy” na ƙasa.
Commodore Adams-Aliu ya ce “irin wannan gaggawar amsawa ga kiran gaggawa na nuna cikakkiyar jajircewar Sojojin Ruwa wajen kare masu zirga-zirga na halal a teku.”
Ya ƙara da cewa, rundunar za ta ci gaba da haɗin gwiwa da ƙasashen yankin don ƙarfafa tsare-tsaren tsaro da tabbatar da cewa Tekun Guinea ya kasance cikin kwanciyar hankali.
Wannan aikin ceto na baya-bayan nan, a cewar rundunar, wani ɓangare ne na sabon tsarin aiki da ya haɗa da sa ido, sintiri, da atisayen gaggawa — tsarin da ya riga ya ceci rayuka da dama a cikin ’yan shekarun nan.
Sojojin Ruwa sun jaddada cewa ƙarƙashin jagorancin Vice Admiral Abbas, ba wani kiran gaggawa da za a yi musu da ba za su amsa ba, kuma babu wani ɗan teku da za a bar shi cikin hatsari a cikin ruwannin Nijeriya.
