
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Gwamnatin Nijeriya ta yi ƙi amincewa da ayyana ƙasar Somaliland a matsayin yanki mai cikakken ƴanci daga ƙasar Somaliya da Isra’ila ta yi a kwanan nan, inda Nijeriyar ta bayyana hakan a matsayin yunƙurin barazana ga ikon Somaliya da yiwuwar aukuwar rashin zaman lafiya a ƙasar.
A wata takarda da Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Nijeriya, Kimiebi Ebienfa ya fitar a jiya Asabar, Gwamnatin Tarayya ta ce za a ta cigaba da ƙoƙarin kiyaye sharuɗɗan iko, iyakance guraben iko da kuma ƴancin siyasa kamar yadda sashen Majalisar Ɗinkin Duniya na ‘Charter of the United Nations’ da dokokin mashawartan ƙungiyar ƙasashen Afirka suka bayyana.
A cewar sanarwar, Nijeriya za ta bada cikakken agaji ga iko, haɗin kai, zama ƙasa na Jamhuriyar Tarayyar Somaliya, domin gwamnatin da ke Mogadishu ita ce halastacciya da ke wakiltar al’ummar ƙasar.
Akan haka Nijeriya ta yi alla-wadai da dukkan wani mataki na yunƙuri rage martabar ikon kundin dokokin Somaliya, tana mai gargaɗin ayyana kowane yanki na ƙasar a matsayin mai cin gashin kansa ba abin da zai haifar sai fargaba da tsananta halin ɗaiɗaita da ake ciki.
Sannan, gwamnatin ta kuma kirayi Isra’ila da sauran ƙasashe da su girmama ikon Somaliya tare da tallafa wa cibiyoyinta a ƙoƙarinsu na sake gina ɗorewa da haɗaɗɗiyar ƙasa.
Haka kuma, gwamnatin Nijeriyar ta gargaɗi ƙasashe a matakin nahiya da ma duniya baki ɗaya da cewa su girmama ikon ƙasar tare da ƙaurace wa ayyukan wani sashinta a matsayin yanki mai cin gashin kansa.
To saidai kuma a wani labarin, ƙasar Somaliyar ta mayar da martani a fusace bayan da Isra’ila ta zama ƙasa ta farko a duniya da ta amince da Somaliland a hukumance a matsayin ƙasa ƴantacciya.
Firaiminista Hamza Abdi Barre, ya ce Somalia ta yi watsi da abin da ya ce hari da gangan da Isra’ila ta kai a kan yancin ƙasarsu.
Firaiministan Isra’ila Benjamin Netanyahu, ya ce gwamnatinsa ta amince za ta faɗaɗa danganta da haɗin kai da Somaliland ɗin a ɓangaren noma da lafiya da kuma fasaha.
Tuni dai shugaban Somaliland Abdirahman Mohammed Abdullahi, ya yaba da wannan ci-gaba inda ya bayyana shi a matsayin tarihin da ƙasarsa ba za ta taɓa mantawa da shi ba.
Ƙungiyar tarayyar Afirka dai ta yi watsi da duk wani yunkuri na amincewa da yankin Somaliland ɗin a matsayin kasa mai ‘yanci inda shugaban ƙungiyar ya yi gargaɗin cewa irin wanann mataki da Isra’ilan ta ɗauka zai iya kawo illa ga zaman lafiyar nahiyar.
