Hukumar NIRSAL ta kammala wani horo ga manoma a kan harkar rogo da kiwon cikin ruwa a jihohin Sokoto, Imo,Kwara da Oyo.
Wannan shirin an yi shi ne domin ƙara wq manoman sani a kan yadda zasu samu bashi da kuma hanyar biya. Shirin ya samu aƙalla manoma 2000 da suka halarta tare da jami’an gwamnati.
Ciyaman ɗin kwamitin noma na majalisar Imo, Mr Uche Agabige ya jinjinawa NIRSAL da ta sanya jihar ta Imo a wannan zagayen horon ga manoman.
A jihar Imo, akwai aƙalla mutane 500 daga wajen horo biyu da aka tanada, ɗaya a cikin birni sai ɗaya a cikin ƙauyuka.
Haka abin ya wakana a sauran jihohin da wannan horon ya faru, inda ana sa ran waɗanda a ka horar za su horar da manona sama da 6000 cikin al’ummar su daga jihohin su.
