Kwastom za su buɗe shigo da abinci daga Ƙasashen waje sati mai zuwa

Spread the love

Hukumar Kwastam ta Najeriya ta sanar da cewa dokar ɗage haraji kan kayayyakin abinci da magunguna za ta fara aiki a mako mai zuwa.

Sanarwar ta fito ne daga bakin shugaban hukumar Kwastam Bashir Adeniyi a wata hirarsa da manema labarai.

Hakan na nufin masu shigo da kayayayyakin abinci kamar shinkafa, alkama, masara, dawa da sauran hatsi, ba za su biya haraji ba har tsayin watanni uku.

Wannan tsarin ya biyo bayan kudirin gwamnatin shugaban Tinubu na rage farashin kayan abinci don rage wa ‘yan kasa raɗaɗin tattalin arziki.

By ukarofi