Zanga-zanga ce mafita?

Spread the love

Gaskiyar magana an samu rabuwar kawuna tsakanin ‘yan Nijeriya musamman ‘yan arewa kan zanga-zanga ta hanyar fitowa ko yin haƙuri. Babban abu shi ne nazarin abun da zai zama mafita ga ƙasa. An samu jan hankali daga ɓangarori daban-daban kan illar da zanga-zanga cikin fushi ko rashin tsari kan iya haddasawa  don kar ya zama garin gyaran gira a tsakale ido. Haƙiƙa wasu matasa sun dau zafi ainun ta yadda in ba ka ƙarfafa a fito zanga-zanga ba ba sa ganin ka na da tausayi ko ma sauran imani. Duk al’ummar da ba ta da maganata to ta kan iya faɗawa gallafiri da rashin tabbas. 

Yaƙi da yunwa ko rashin samun shugabanci mai kyau kan cimma buri ta hanyar zanga-zanga? Wasu sun dau amsar cewa zanga-zanga ne yaren da gwamnati ke ji. A nan za mu ce wace gwamnatin a ke magana ta dimokuraɗiyya ko ta soja ta Afurka ko ta asar Turai ko Larabawa. Duk matakin da matasa su ka zaba an riga an yi magana a kai. Ni abun da na lura da shi matasa ba sa amincewa da jan hankali sai bayan sun jarraba sun ga amfanin abu ko akasin hakan. 

Mutane da dama sun mara baya ga zanga-zangar yaƙi da zaluncin ’yan sandan SARS kuma gaskiya ne gwamnati ta yi gyaran fuska ga irin waɗannan ’yan sanda masu wuce gona da iri amma haƙiƙa in an duba wasu sun yi amfani da damar a lokacin wajen maida zanga-zangar dandalin faɗan addini da ɓangaranci inda a ka samu asarar rayuka da dukiya mai yawan gaske da har zuwa yau ba a samu diyya ko maye gurbin abun da a ka rasa ba. Waɗanda su ka mutu ’yan uwan su sun rasa su haka nan waɗanda su ka yi asarar dukiya da motocin dakon kaya na arewa a kudu su ma haka su ka haƙura don  lamarin ya afku a inuwar zanga-zanga ne. A lokacin ne ma wasu su ka buɗe wuta a Jos su ka samu tsakiyar kan dan marigayi ɗan jarida Aminu Ahmed Manu na gidan rediyon Faransa. Matashin ya na anguwar su a ka kashe shi a rububin zanga-zanga.

 Ko kadan ba wanda zai ƙi marawa zanga-zanga baya matuƙar za a gudanar da hakan lami lafiya ta hanyar bayyana muradu da mutunta juna. Ko zanga-zangar da ta afku a zamanin mulkin tsohon shugaba Jonathan da a ka ce an samu nasara ta afku ne a tsare ƙarƙashin ƙungiyar ƙwadago ta NLC da TUC kuma a keɓantattun wajaje bisa jagoranci. Irin wannan zanga-zanga da ta faro daga kamfen na yanar gizo da wasu zarge-zarge na wasu muradu za ta iya kawo firgici ga mutane da ke hangen ba za a wanye lafiya ba. Mu na fatan Allah ya kawo mafita ga Nijeriya da ’yan Nijeriya. Gwamnati a na ta ɓangare ta ɗau ƙarin matakan da za su kawo sauƙi ga al’ummar ƙasa su kuma al’umma su riƙa kaucewa rabuwar kawuna ta dalilan bambancin addini, ƙabila, yanki ko siyasa. Duk abun da za a gudanar ya zama ba wata ɓoyayyiyar manufa ta son zuciya a ciki. Dama kusan duk ɓangarorin Nijeriya na fuskantar wani ƙalubale ta ɓangaren tsaro. Arewa maso Gabas na da sauran fafutuka da ‘yan Boko Haram. Arewa maso yamma ga ɓarayin daji da kamfen din neman ƙirƙiro tsamar ƙabilanci. Arewa ta tsakiya nan ma ga ɓarayin na daji da tsamar bambancin addini.

 Kudu maso gabar ga ’yan awaren Biyafara na IPOB da kan kashe musamman jami’an tsaro. Kudu maso kudu ga ɓarayin man fetur. Kudu maso yamma a na ta buga gangunan ƙasar Oduduwa. Kun ga kasa mai irin wannan ƙalubale a kowane ɓangare na fafutukar zama tare bisa jagorancin gwamnatin tsakiya ne da duk wata fitina ka iya ɗaukar wani salo da ba zai haifar da alheri ba.

Masu sharhi da kuma wasu shugabannin al’umma na bagyana mabanbantan ra’ayi kan shirin zanga-zangar matasan Nijeriya don nuna damuwa kan tsadar rayuwa.

Wannan na zuwa ne gabashin ranar Alhamis ɗin nan wato ɗaya ga watan Agusta da matasan su ka ayyana don zanga-zangar.

Shaharerren malamin Islama Dr.Ahmad Gumi wanda a farko ya ce zanga-zanga ce yaren da gwamnati da gwamanti ke ji; a yanzu ya buƙaci matasan da su jinkirta zanga-zangar.

A zantawa da Muryar Amurka, malamin ya ce saƙon matasan ya isa ga gwamnati “ina ganin saƙon su ya isa inda ya kamata ya isa. Ina ba su shawara domin maslahar kan su kafin wani sannan kua maslahar al’umma gaba ɗaya su janye maganar wannan zanga-zanga gaba ɗaya su ba da wata 6 ma na har zuwa Janairu su gani in gwamnati ba ta yi wani abu ba sannan sai su yi tsari tsarin da za a tabbatar ba a cutar da kowa ba an yi zanga-zanga na lumana”

Shi kuma shugaban ƙungiyar makiyaya ta MIYETTI ALLAH Baba Usman Ngelzarma ya shawarci matasan su janye zanga-zangar don alamun ba za ta haifar da alheri ba.

Tsohon kwamishinan kasuwanci na jihar Sokoto Aminu Bello ya yi kira ga gwamnati ta amsa wasu buƙatun matasan don dakatar da shirin “gwamnati mu na kira gare ta ta duba ba wai a cire (subsidy) ba a’a a tsaya a rage kuɗin mai kuma a rage dala a rage haraji, to idan a ka yi haka kowane ɓangare za a samu sauƙi”

A nasu ɓangaren shugaban gamayyar ƙungiyoyin arewa Jamilu Aliyu Charanci ya yi gargaɗin a kwantar da guguwa mai tinkarowa kar ta kai ga juyin juya hali “ganin irin yadda hadari ke tattaruwa a ƙasar ya yi baki kwarai; abun da ya rage haɗarin nan ya tsage ruwa ya zuba ƙasa. To kamar mace ce gurguwa wadda a ka kama kafar ta guda a ka karya. Kai da a ke tsammani za ka ɗaura ƙafar sai ka zo ka ida samun kafa guda ka ida karya ta”

Yanzu dai da alamun wasu matasan sun janye daga zanga-zangar inda wasu ke cewa ba gudu ba ja da baya.

Tsohon ɗan majalisar wakiali Muhammad Gudaji ya bayyana cewa  masu shirya zanga-zanga musamman a arewacin Nijeriya sun tuntube shi don shiga tsakanin su da gwamnati.

Kazaure ya ce ’yan bindigar sun zabe shi da mutum biyu da su ka haɗa da Farfesa Attahiru Jega da Kanar Dangiwa Umar.

Kazaure ya ce sun shimfiɗa sharuɗɗa 10 na dakatar da zanga-zangar da su ka haɗa da dawo da tallafin fetur da janye ƙarin kudɗn wuta, gude kan iyaka da sauran su.

Gudaji Kazaure ya ce idan gwamnati ta amince sai a dakatar da zanga-zangar zuwa kwana 60 don ganin amsa buƙatun a zahiri.

ɗan majalisar ya nuna fargabar har a ka bari a ka tafi zanga-zangar akwai hatsari ainun wajen dukiyar jama’a da dimokraɗiyya.

Masu zanga-zangar nuna damuwa kan auncin rayuwa a Nijeriya sun datse hanyar Abuja daga babban titin da ya taso daga Kaduna.

Wannan dai na faruwa ne kwana 3 gabanin ranar Alhamis da matasa su ka ayyana za su fara zanga-zangar.

Masu zanga-zangar na riƙe da kwalaye na nuna rashin jin daɗi da tsadar rayuwa da kuma caccakar gwamnatinTinubu kan halin da a ke ciki.

Ba mamaki fara zanga-zangar da wuri ya sa a ka ga jami’an tsaro cikin Abuja don ɗaukar matakan hana karya doka da oda.

Sarakunan kudu maso gabashin Nijeriya sun ce ba sa goyon bayan shirin matasa na gudanar da zanga-zanga a farkon watan gobe.

Shugaban majalisar sarakunan yankin Igwe Samuel Asadu na masarutar Ogwugwu a Nsukka da ke jihar Enugu ya baiyana matsayar a taron kamfanin dillancin labaru na Nijeriya NAN.

Igwe Asadu ya ce miyagun iri ka iya shiga cikin zanga-zangar su haddasa fitina don haka ya buƙaci matasa su janye shirin na su.

A nan Igwe ya shawarci shugaba Tinubu ya saurari matasan don su na da ƙorafin su a yanayin wuyar rayuwa da ƙasa ke ciki.

Kazalika basaraken ya buƙaci saƙo shugaban ƙungiyar IPOB ta rajin kafa Biyafara Nnamdi Kanu da nuna hakan zai kawo sauƙin ƙalubale a yankin.

Hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta bayyana cewa ta gano masu ɗaukar nauyin zanga-zanga kuma su na yin hakan ne don tada fitina.

Daraktan labaru na hukumar ta DSS Peter Afunanya ya fitar da bayanan a cikin wata sanarwa.

DSS ta ce ‘yan ƙasa su na da hurumin yin  zanga-zangar lumana amma masu wannan shirin a farkon watan gobe na da mummunar manufa.

Hukumar ta zargi masu shirya zanga-zangar da neman cimma muradun siyasa wajen neman kifar da gwamnati mai ci.

Kazalika DSS ta ce akwai masu son amfani da damar zanga-zangar wajen kutsawa ciki su kawo hatsaniya ga kasa.

Madugun shirya zanga-zanga ta matasa Komred Murtala Garba ya ce masu yayata hoton sa da na ɗan shugaba Tinubu wato Seyi na neman bata ma sa suna ne.

Komred Garba dai tun farko ya fito ya janye kan sa da jama’ar sa daga shiga zanga-zangar da nuna cewa akwai lauje cikin naɗi.

Garba ya ce hoton da a ke yayatawa tsoho ne tun zamanin kamfen din 2023 kuma wannan sam ba ya nuna wata alaƙa da gwamnati.

A nan Garba ya ƙara nanata cewa zanga-zangar da a ke son shiryawa akwai matsalar neman tada fitina a yankin arewa.

Kazalika Garba ya yi kira ga gwamnan Filato da na Kaduna su ɗau matakai na tabbatar da zaman lafiya a jihohin su.

Kammalawa;

Shugaban ƙungiyar JIBWIS Imam Abdullahi Bala Lau ya ce sun isar da saƙon al’umma na ƙuncin rayuwa ga shugaba Tinubu.

Shehun malamin na magana ne bayan kammala ganawa da shugaba Tinubu da malaman Islama su ka yi a fadar Aso Rock.

Sheikh Bala Lau ya ce sun shaidawa shugaban damuwar jama’a kuma ya nuna aniyar ɗaukar matakai don magance matsalolin.

Malamin ya buƙaci musulmi da Kirista su yi haƙuri su yi addu’a ga shugaban aasa da ƙasar don samun sauyi a yanayin rayuwar da a ke ciki.

Malaman sun buƙaci matasa masu niyyar yin zanga-zanga don ƙuncin rayuwa su yi haƙuri su janye hakan don ganin abun da gwamnati za ta yi.

By ukarofi