NITDA ta buɗe cibiyar tsaro ta yanar gizo a Kano 

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Hukumar Bunƙasa Fasahar Sadarwa ta ƙasa (NITDA) ta ƙaddamar da Cibiyar Tsaron ta yanar-gizo ta ƙasa  a Jami’ar Bayero da ke Kano (BUK), a  wani muhimmin mataki wajen ƙarfafa bunƙasa tsaro ta amfani da fasahar zamani da ci gabansa a Nijeriya.

An ƙaddamar da cibiyar ne a ranar Talata, 20 ga Mayu, 2025, inda Darakta Janar na NITDA, Kashifu Inuwa Abdullahi, CCIE, ya samu wakilcin Shugaban Ofishin  NITDA, shiyyar Arewa Maso Yamma, Dr. Jide Ajayi. 

A jawabinsa, Dr. Ajayi ya bayyana cibiyar a matsayin wata muhimmiyar kadarar ƙasa da aka kafa domin bunƙasa ilimi, bincike da ƙirƙire-ƙirƙire a fannin tsaron intanet, cikin daidaito da manufofin “Renewed Hope” na Shugaba Bola Ahmed Tinubu da kuma tsare-tsaren dabarun Ministan Sadarwa.

A nasa jawabin, Shugaban Jami’ar Bayero, Farfesa Sagir Adamu Abbas, ya nuna gamsuwa da godiya ga NITDA, yana mai cewa wannan cibiyar ta zo a daidai lokacin da ya dace.

Ya bayyana cewa jami’ar tana gudanar da shirye-shiryen karatun digiri na BSc da MSc a fannin Tsaron Intanet, kuma tana shirin ƙaddamar da shirin Digiri na uku (PhD) a fannin, domin tabbatar da BUK a matsayin cibiyar bunkasa kwarewa a bangaren tsaron intanet a ƙasa baki ɗaya.

A ci gaba da ƙoƙarinta na inganta tsaron intanet a ƙasa, NITDA ta sanar da shirinta na gudanar da Taron Tsaron Intanet na ƙasa da za a gudanar a ranar 9 zuwa 10 ga Yuli, 2025 a birnin Abuja. Za a shirya taron tare da Ofishin Mai Bada Shawara Kan Harkokin Tsaro, inda za a haɗa masana daga sassa daban-daban na duniya, masu tsara manufofi da masu ƙirƙire-ƙirƙire don tsara makomar fasahar zamani mai cike da tsaro da ingantaccen amfani da fasahar AI a Nijeriya.

By ukarofi