Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Shugaban haramtacciyar ƙungiyar IPOB, Mista Nnamdi Kanu, ya kori dukkan lauyoyinsa tare da bayyana cewa zai kare kansa da kansa a gaban kotu.
Kanu ya bayyana hakan ne a lokacin zaman kotu yayin da yake shirin fara kare kansa kan tuhumar da gwamnati take masa kan cin amanar ƙasa.
A lokacin zaman kotun da aka gudanar a ranar Alhamis, babban lauyan Kanu, Sanata Kanu Agabi (SAN), ya sanar wa kotu cewa shi da sauran manyan lauyoyin Kanu sun janye daga kare shi a wannan shari’ar.
Mai shari’a James Omotosho ya amince da buƙatar janyewar lauyoyin.
Bayan haka, alƙalin ya tambayi Kanu ko yana da sabon lauya da zai kare shi, sai Kanu ya amsa da cewa: “Zan tsaya da kaina na kare kai na, bana buƙatar lauya.” Daga nan sai Mai shari’a Omotosho ya umurci sauran ƙananan lauyoyin da su bar ɗakin kotu.
A halin yanzu, labari na cewa Nnamdi Kanu ya saka sunayen tsofaffi da kuma wasu jami’an gwamnati masu aiki a matsayin shaidu da zai gabatar wajen kare kansa.
Cikin jerin sunayen da ya ambata akwai tsohon babban lauyan gwamnatin tarayya, Abubakar Malami; tsohon babban hafsan sojojin Nijeriya, Janar Tukur Buratai; tsohon Ministan Tsaro, Janar Theophilus ɗanjuma; da kuma gwamnonin jihohin Legas da Imo — Babajide Sanwo-Olu da Hope Uzodinma, tare da wasu mutune da dama.
