
Daga BELLO A. BABAJI
Gidajen man fetur mallakar kamfanin NNPCL, sun ƙara farashin kowacce lita a jihohin Abuja da Legas.
Kafin yanzu, ana sayar da litar ne akan N897 wanda yanzu kuma an mayar da shi zuwa N1,030 a Abuja.
A yankin Maitama da ke Abuja, an ruwaito cewa mutane sun yi cincirindo wajen sayan man inda suke ta ƙorafi game da ƙarin.
‘News Point Nigeria’ ta ruwaito cewa masu sayan man sun ɗauki tsawon lokaci su na jira don a fara sayar da man a yankin Gudu na Abuja inda wani ma’aikaci ya ce ana aikin mayar da na’urar ne zuwa sabon farashin kafin a fara sayarwa.
Haka ma, a Legas da ake sayarwa akan N885, yanzu an mayar da shi N998 inda ake samun dogayen layuka a gidajen man.
Hakan na zuwa ne jim-kaɗan bayan janyewa daga dillanci da NNPCL ya yi a harkar sayan mai daga matatar Ɗangote wanda hakan ya bai wa ƴan kasuwa damar saya kai-tsaye.
