Tun Ina firamare na fara rubutu
Daga UMAR GARBA, a Katsina
Zaidu Ibrahim Barmo matashi ne da ya yi fice a fannoni daban daban, kama daga rubutun litattafai ko labarai a mujallu da jaridu gami da yin sharhi game da rayuwar matasa a kafafen yaɗa labarai. Kazalika matashin shine mamallakin fitaccen shafin nan na Mujallar Zauren Marubuta da ke wallafa abubuwan da suka shafi marubuta ko ‘yan fim dama sauran al’umma bakiɗaya a dandalin Facebook.Wakillin Manhaja a Katsina ya tattauna da Zaidu Ibrahim Barmo, a kan abubuwan da suka shafi aikace aikacensa, alaƙarsa da marubuta, shawara ga matasa, ƙalubalen da yake fuskanta gami da nasarori da ya samu a rayuwarsa.
MANHAJA: Masu bibiyar Blueprint Manhaja za su so jin taƙaitaccen tarihinka?
ZAIDU: Sunana Zaidu Ibrahim Barmo, ni ɗan ƙaramar Hukumar Jibia ne a Magama, amma yanzu Katsina nake zaune.
Na yi karatun firamare a Kaga Jibrin Primary School da ke Magama, amma secondary na yi mabambantan makarantu ta ƙarshe na gama a Goɓernment Science Secondry School da ke Magama.
Bayan na kammala na shiga cibiyar samarwa matasa aikin yi ta ƙasa wato ‘National Directorate of Employment NDE, inda na yi karatu akan Computer har zuwa watanni shida.
Daga nan na shiga Kwalejin horas da malamai da ke Katsina wato ‘Federal College of Education Katsina’ inda na karanta ‘Hausa Social Studies.’
A shekarar 2019 ya kamata ace na gama, amma saboda kullen ‘Corona’ ban gama ba sai a shekarar 2020.
Ni ne mai shafin Mujallar Zauren Marubuta da ke a dandalin Facebook.
Yaushe ka kafa mujallar zauren marubuta?
An kafa Mujallar Zauren Marubuta a shekarar 2017, a lokacin babu wani shafi a Soshiyal Midiya da yake magana akan marubuta, saboda haka sai naga har waɗanda ba su kai matsayin a kira su marubuta ba, suna da shafin da suke saka ayyukansu, misali duk wani abu daya dangacesu za ka gani a wajan amma marubuta ba su da shi, kuma ina da burin fito da matasa masu baiwa haka irin haka, waɗanda duniya bata san da su ba dan nunawa al’umma irin fasahohin su, daga nan na ce to bari ƙirƙiri shafin ya zamo duk wani abu daya danganci marubuci zaka ganshi a Mujallar zauren marubuta, walau aure, suna biki ko kuma mutuwa duk za a sanar a shafin na sada zumunta.
Sai dai daga baya na faɗaɗa shafin ya zama ba marubuta kaɗai ba har kowa ma zai iya zuwa.
Shiyasa yanzu shafin ya zama na kowa da kowa, tun daga matasa, dattijai da kowane ɓangare na al’umma.
Ana ganinka tare da marubuta shin kai ma marubuci ne?
Sosai ma kuwa ni ma marubuci ne Mallam Umar, na fara rubutu tun Ina ‘Primary School,’ lokacin irin za ka yi jagwalgwalo da sunan rubutu, misali zan yi zane a littafina wato ‘Eɗercise Book,’ na kan zana ‘Cartoon’ da sunan ni ma nan littafi ne na rubuta, har dai ta kai zuwana sakandare inda na fara rubuta cikakken littafi.
Sanadiyyar shiga ta ƙungiyar marubutan Katsina KMK, ya sa na san marubuta da yawa, wasu kuma a dandalin Facebook na sansu irin waɗanda ba ‘yan Jihar Katsina ba.
A cikin rubuce rubucen da ka yi wane littafi ko labari ya fi shahara?
Na yi rubutun litattafai zasu kai guda goma sha biyar, amma cikin litattafan da na rubuta mutane sun fi son labarin “Mutumin Facebook” wanda yanzu haka an sa yi labarin don a mayar da shi fim ɗin Hausa.
Ko za ka ɗan yi wa masu bibiyar Manhaja tsokaci game da jigon labarin?
Labarin ‘Mutumin Facebook’ labari ne akan wani matashi na gina labarin da sigar akan kaina ya faru, amma ba da gaske ba ne jan hankali ne dan mutane su hankalta, kan yadda mutane suka maida rayuwarsu kan Facebook, wani ko ruwa zai sha sai ya ɗora a Facebook, wani tafiya zai yi nan da nan sai an san inda yaje, sai ya zamo cikin sauƙi mutane na iya gane inda kake rayuwa, yanayin da kake ciki, na daɗi ko akasin haka, abinci da kayan da kake so dai duk mutane sun sani sanadiyyar komai namu ba a ɓoye yake ba, muna bayyanawa, to a haka ne tauraron labarin ya haɗu da wani ɗan damfara, da bai shigo rayuwarshi ba sai da ya gama sanin shi ciki da waje sanadiyyar Facebook, da haka ya yi amfani da wannan damar ya damfare shi, ya kuma yi mashi yawo da hankali ba kaɗan ba.
Ina son nuna wa mutane mu rage fadin wasu abubuwa da suka danganci rayuwarmu a dandalin Facebook, saboda Facebook ya wuce duk tunaninmu, abu kaɗan za ka yi yanzu duniya zata ɗauka sanadiyyar Facebook.
Duba da muhimmancin jigon labarin ne marubuci Bala Anas Babinlata yaga labarin, ya haɗani da wani darakta ya sayi labarin zasu mayar da shi fim.
Mafi yawan marubuta a halin yanzu sun koma rubuce rubuce a shafukan soshiyal midiya. A ganinka me ya sa suka zaɓi yin rubutu a shafukan sada zumunta fiye da yadda aka saba gani a baya wato rubutun littafi?
Zamanin ne ya koma haka, mutane yanzu ba su da ɗabi’ar karatu don haka in ka cewa mutum ya ɗauki littafi ya karanta zai ga ka sara mashi aiki, ƙila hidindimun da ke kanshi kaɗai sun ishe shi.
Amma wayar shi ko yaushe tana hannun shi, don haka fara rubuce rubuce a soshiyal midiya ya taimaka wa marubuta da yawa wajan yin rubutu a online, ya kuma sauƙaƙawa makarantan yin karatun ba tare da takura ba.
Saboda dama marubuci saƙo yake son isarwa don haka in dai za a ji saƙon shi ko a takarda, ko a doshiyal midiya duk ɗaya ne.
Ko akwai wasu shirye shirye da kake yi don ganin ka haɓɓaka shafin mujallar zauren marubuta fiye da yadda yake a halin yanzu?
Sosai ma kuwa, kamar a baya iya online ne kawai muke posting a ‘Facebook Page’ ɗinmu, amma a wannan shekarar mun fara buga Mujallar Zauren Marubuta bugun farko, shi ne ma muka ƙaddamar a wajen taron wannan shekarar.
Sannan akwai shirye shiryen da a baya bama yin su, amma yanzu ana yi, sannan Ina ta tunanin ƙirƙiro da wasu sabbi waɗanda daga mu ne kaɗai za a dinga ganin su.
Banda harka rubutu ko tafiyar da shafinka na Mujallar Zauren Marubuta, ko akwai wata sana’a da kake yi?
E, Ina da ‘MrZaid Uniƙue Collection’ da nake sayar da kayan sakawa da suka danganci huluna, shaddodi, yadiddika, akwatunan lefe da dukkan kayan buƙata dai na jiki na maza da mata na duttura, sannan Ina sayar da tea spices wato kayan haɗin shayi.
Wacce shawara za ka bai wa matasa akan su dage su nemi na kansu?
Ina ba su shawara da su yi ƙoƙari su nemi na kansu, yau da daɗi ace kana yiwa kanka abu ba tare da ka jira anyi maka ba, yafi ace kai ke bayarwa da ace kai ake ba, sannan daga cikin muhimmancin neman na kai akwai rufawa kai asiri, ta yadda wani ba zai taɓa jin kukanka ba.
Sannan mutane za su kalle ka da mutunci, idan mutum na sana’a ko waje yaje ana girmama shi, saboda ana mashi kallon wannan fa ba ‘Liability’ ba ne.
Sannan idan kana neman na kanka zai sa ka yiwa ‘yan uwanka abinda ba zaka zuba ido kana ji kana gani wani yai masu a waje ba musamman mata.
Wane ƙalubale kake fuskanta a yayin gudanar da aikinka?
ƙalubalen ba mai yawa ba ne gaskiya saboda kaga komai a online ne, amma wani lokacin neman rubutun da zaka saka ya ɗauki hankalin jama’a sai ya zama aiki, ga shi dai kana son nemo labari amma ya yi wahala, ko kuma ka yi posting ɗin bidiyo kana son mutane su kalla, amma Facebook su riƙe bidiyon, kuma ƙila biyanka aka yi ka saka bidiyon, to kaga wannan ƙalubale ne tunda wanda ya baka tallar in bai samu abinda yake so ba, ba zai dawo wajenka gobe ba.
Waɗanne nasarori ka samu a rayuwa?
Gaskiya Alhamdulillahi ! Na samu nasarori da yawa, amma nasarar farko da nake kallo ita ce, buɗe shafin Mujallar Zauren Marubuta, saboda dalilin shi ne na haɗu da mutane da yawa, waɗanda ban taɓa tunanin shekaruna ko rubutuna zai kaini wajen su ba, sannan mutane sun sanni sosai, ko wuri naje sai naga ana girmamani, wani ma ban taɓa ganin shi ba amma da mun haɗu zaka ji ya ce “CEO” Sai kaji mutum ya ce ai ina following ɗinka a Mujallar Zauren Marubuta.
Bayan nan na sha samun gayyatar tarurruka daga ƙungiyoyin da ba dan ƙila an sanni ba, da ba zan je wajen su ba.
Sannan kaga yau kana yiwa kanka komai ba tare da jiran ayi maka ba, shima babbar nasarar rayuwa ce.
Mun gode sosai Mallam Zaidu da lokacinka da ka ba mu.
Ni ma na gode da wannan tattaunawa da ka yi da ni Mallam Umar, kuma ina godiya ga jaridar Manhaja bisa samun damar tattaunawa da n
