Yan bindiga sun kashe Sarkin Kanya a Jihar Kebbi

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

‘Yan bindiga sun kashe Sarkin Kanya Alhaji Isah Akiyu, na ƙaramar hukumar Danko Wasagu a Jihar Kebbi bayan sun yi garkuwa da shi.

‘Yan bindigan sun fara neman kuɗin fansa domin sakin Sarkin Kanya.

Duk da ƙoƙarin al’ummar yankin wajen tattaunawa domin dawowarsa lafiya, masu garkuwan sun kashe shi, kisan gilla.

Kisan wannan basaraken gargajiya ya girgiza garin Danko Wasagu da kewaye, yayin da mazauna yankin ke alhini tare da bayyana tsoro game da ƙaruwar ayyukan ‘yan bindiga a Jihar Kebbi.

Mutane da dama sun yi kira ga gwamnati da jami’an tsaro da su ƙara himma wajen yaƙar wannan matsalar rashin tsaro da ke ƙara kamari, musamman kai hari kan shugabannin al’umma da fararen hula.

Wannan al’amari ya ƙara bayyana matsalar garkuwa da kashe-kashe da ‘yan bindiga ke aikatawa a Arewacin Najeriya, inda ‘yan bindigan ke ci gaba da tarwatsa rayuwar al’ummomin yankin.

By ukarofi