NNPC ya sake rage farashin fetur kwanaki biyu da hauhawarsa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Babban Kamfanin Fetur na Ƙasa (NNPCL) ya rage farashin lita a gidajen mansa kwana biyu da tashinsa a kasuwa.

Blueprint ta ruwaito cewa, an koma sayerwa akan N900 daga N955 a gidajen man, kamar yadda aka gani a yankunan Gwarimpa, Kubwa, Wuse Zone 6 da Wuse Zone 4 da ke birnin tarayya Abuja.

Hakan ya nuna an samu ragin N55 ga kowace lita bayan da farashin ya koma N955 a ranar Litinin.

Haka ma a wasu gidajen mai na ƴan kasuwa irin su Ranoil da Empire Energy da ake sayerwa a N950 da N955 daga N971 da N970 a baya.

By Babaji