Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Kamfanin Mai na ƙasa (NNPC), ya fara ɗaukar matakan sayar da wani kaso na hannun jarinsa a wasu kadarorin mai da gas, a wani yunƙuri na sake tsara harkokinsa tare da jawo sabbin masu zuba jari zuwa ɓangaren mai na Nijeriya.
Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da NNPC ke fuskantar manyan ƙalubale na aiki, raguwa a zuba jari, da kuma ƙaruwar buƙatar jari domin ƙara yawan haƙo mai da gas.
Masana na ganin wannan shiri na daga cikin manyan dabarun da kamfanin ke bi domin sauya salo daga tsohuwar hanyar gudanarwa zuwa tsarin kasuwanci na zamani.
Wata takardar gayyata da aka fitar a farkon makon nan, ta nuna cewa NNPC ta buɗe ƙofa ga masu sha’awar zuba jari domin miƙa tayin sayen wasu hannayen jarin da take da su. Sai dai ba a bayyana adadin kaso da za a sayar ko kuma girman kuzin da ake sa ran samu ba.
A cewar rahoton Reuters, “NNPC, kamfanin mai da gas mallakin gwamnatin Nijeriya, na shirin sayar da wasu hannayen jarinsa a kadarorin mai da gas, kuma ya gayyaci masu zuba jari su shigar da tayinsu.”
A halin yanzu, NNPC na da hannayen jari a kadarori da dama na mai da gas, ciki har da mallaka kai tsaye da kuma haɗin gwiwa da manyan kamfanonin ƙasa da ƙasa kamar Shell, Cheɓron, Eni da TotalEnergies. Wannan ya sa shirin sayar da wasu kaso ke da matuƙar tasiri ga gaba ɗayan ɓangaren makamashi na ƙasar.
Takardar gayyatar ta bayyana cewa an tsara tsari mai matakai da dama. Za a fara ne da rajistar masu sha’awar zuba jari ta yanar gizo kafin ranar 10 ga Janairu, sannan a yi tantancewar farko. Waɗanda suka tsallake wannan mataki ne kawai za su samu damar shiga wani dakin bayanai na musamman a yanar gizo, inda za su duba cikakkun bayanan fasaha, kuɗi da tsarin gudanarwa na kadarorin da ake shirin sayarwa.
A cewar bayanan, za a yi la’akari da ƙarfin fasaha da ikon kuɗi na kamfanonin da ke neman sayen hannayen jarin. Bayan haka, za a shiga matakan tattaunawa, tantance takardu da kuma neman amincewar hukumomin da abin ya shafa.
Wannan shiri ya yi daidai da bayanan baya da NNPC ta taɓa fitarwa, inda ta nuna niyyar sayar da aƙalla kashi 25 cikin 100 na wasu filayen mai da gas, ko dai ta hanyar sayarwa gaba ɗaya ko rage hannun jarinta. Sai dai a wancan lokaci, ƙungiyoyin ma’aikatan ɓangaren mai sun nuna tsananin adawa, suna nuna damuwa kan yiwuwar rasa ayyukan yi da kuma tasirin shirin ga muradun ƙasa.
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, NNPC ba ta bayar da wata amsa ba kan buƙatar karin bayani dangane da wannan sabon mataki na gayyatar masu zuba jari.
Nijeriya, wadda ita ce babbar mai hako mai a Afirka, ta shafe shekaru tana fama da matsalolin kara yawan fitar da mai, tare da faɗuwar amincewar masu zuba jari sakamakon rashin tabbas na dokoki, satar mai, lalata bututun mai da kuma tsufan kayayyakin aiki. A ‘yan shekarun nan, ƙasar ta fi dogaro da ƙananan filayen mai na cikin gida domin ci gaba da samar da kuɗaɗen shiga.
Masana na ganin cewa idan aka aiwatar da wannan shirin yadda ya kamata, zai iya zama wata sabuwar hanya ga NNPC wajen zama kamfani mai cin gashin kansa a kasuwanci, tare da aika saƙo mai ƙarfi ga masu zuba jari cewa Nijeriya na ƙara bude ƙofa ga jarin ɓangaren mai da gas.
