Otedola ya sayar da hannun jarinsa a Geregu Power kan Naira tiriliyan 1.1

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Attajirin ɗan kasuwa, Femi Otedola, ya sayar da mafi rinjayen hannun jarinsa a kamfanin Geregu Power Plc a wata babbar yarjejeniya da ta kai kimanin Naira Tiriliyan 1.088, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 750.

Wannan ciniki na daga cikin manyan muhimman sauye-sauye da aka samu a fannin lantarki a Nijeriya cikin ‘yan shekarun nan.

Yarjejeniyar, wadda wasu bankuna ƙaraashin jagorancin Bankin Zenith suka ɗauki nauyin kuɗinta, ta shafi sayar da kaso kashi 95 cikin 100 na Otedola a kamfanin Amperion Power Distribution Company Limited, wanda shi ne babban mai riƙe da hannun jari a Geregu Power. Kamfanin MA’AM Energy Ltd, wani kamfani na makamashi da ke Abuja, shi ne ya sayi wannan kaso, lamarin da ya ba shi cikakken ikon sarrafa Amperion.

A cikin wata sanarwa da kamfanin Geregu Power ya fitar ga Kasuwar Hannayen Jari ta Nijeriya (NGX), an tabbatar da sauyin mallaka, inda aka ce MA’AM Energy ya zama sabon mai rinjayen iko a Amperion.

Sanarwar ta ce, wannan sauyi ya kawar da ikon da Calɓados Global Serɓices da Femi Otedola ke da shi a baya kan kamfanin Geregu Power ta hanyar Amperion.

Sai dai kamfanin ya bayyana a fili cewa yarjejeniyar ba ta shafi sayar da hannayen jarin Geregu Power kai tsaye ba. A cewarsa, tsarin rabon hannayen jari na kamfanin a NGɗ bai sauya ba, illa dai an samu canji ne kawai a wajen “ultimate beneficial ownership” na kashi 77 cikin 100 na jarin kamfanin da aka riga aka fitar.

Bayan kammala cinikin, an sanar da sauye-sauye a shugabancin kwamitin daraktocin Geregu Power.

Tsohon gwamnan Jihar Zamfara kuma Sanata, Abdul-Aziz Abubakar Yari, ya zama sabon shugaban kwamitin daraktoci, inda ya maye gurbin Otedola. Haka kuma, an naɗa Abdulkadeer Babangida Njiddah a matsayin darakta mara zartarwa.

Duk da ficewarsa daga shugabancin Geregu Power, Otedola na ci gaba da riƙe muƙamin shugaban First HoldCo Plc, kuma ana sa ran zai fi karkata hankalinsa wajen faɗaɗa jarinsa a ɓangaren bankuna. A halin yanzu, yana da kaso kashi 17.01 cikin 100 a Bankin First, wanda ya sanya shi babban mai riƙe da hannun jari guda ɗaya a bankin, ko da yake har yanzu yana da ƙaramin kaso a Geregu Power.

A lokacin jagorancinsa, an samu gagarumin sauyi a Geregu Power, inda ƙarfin samar da wutar lantarki ya ƙaru daga megawatt 80 zuwa megawatt 435. Wannan ya sauya kamfanin daga wani tsohon ginin samar da wuta zuwa ɗaya daga cikin manyan kamfanonin wutar lantarki masu ƙarfi a Nijeriya.

By ukarofi