’Yan Nijeriya sun yi amfani da terabayit miliyan 1.236 na data a Nuwambar 2025 – NCC

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Amfani da data a Nijeriya ya kai sabon matsayi mafi girma a tarihin ƙasar a watan Nuwamba na shekarar 2025, inda mutane suka kashe kusan terabayt miliyan 1.236 na data, wato kusan petabayt 1.24, a cewar alƙaluman Hukumar Sadarwa ta Nijeriya (NCC).

Wannan shi ne adadin wata guda mafi girma da aka taɓa samu tun bayan fara tattara irin waɗannan bayanai.

Rahotanni sun nuna cewa wannan adadi ya ɗan zarce na watan Oktoba, wanda aka kiyasta ya kai terabayt miliyan 1.235, alamar da ke nuna ci gaba mai ƙarfi duk da matsin tattalin arziki da aka fuskanta a farkon shekarar, da kuma raguwar masu rijista a wasu lokuta.

Wannan ci gaba ya ƙarfafa matsayin Nijeriya a matsayin babbar kasuwar intanet a Afirka.

A tsawon shekarar 2025, an ga hauhawar amfani da data a hankali amma a tsari mai ɗorewa. Daga kusan terabayt 983,000 a watan Afrilu, lokacin da farashin data ya yi tasiri kan masu amfani, amfani da intanet ya riƙa ƙaruwa har ya haura terabayt miliyan 1 a tsakiyar shekara. A watan Yuni an samu terabayt miliyan 1.044, Yuli ya kai terabayt miliyan 1.131 wanda a wancan lokaci ya zama sabon tarihi, sannan Agusta ya haura zuwa terabayt miliyan 1.152.

Masana sun bayyana cewa matsakaicin ƙaruwa daga wata zuwa wata a rabin ƙarshen shekarar ya kai kusan kashi 1.8 cikin 100, sakamakon dawowar masu rijista, faɗaɗa hanyoyin sadarwa na 4G, da kuma tsananin sha’awar jama’a ga kallon bidiyo, kafafen sada zumunta da harkokin kuɗi na zamani. Wannan sabon matsayi ya nuna yadda rayuwar fasahar zamani ke ƙara shiga cikin lamuran yau da kullum na ’yan Nijeriya.

Kamfanonin MTN da Airtel, waɗanda ke riƙe da fiye da kashi 85 cikin 100 na kasuwar sadarwa, su ne suka fi cin gajiyar wannan hauhawa. Alƙaluma sun nuna cewa matsakaicin amfani da intanet ga kowane mai layi ya ƙaru, inda masu amfani da MTN ke kashe kusan gigabayt 13 a wata, yayin da na Airtel ke kusantar gigabayt 10.

Duk da wannan ci gaba, ƙalubale na nan daram. Amfani da fasahar 5G har yanzu bai wuce kashi 3.6 cikin 100 ba, sakamakon tsadar na’urori da matsalolin lasisi. Haka kuma, lalata wayoyin fiber da matsalolin wutar lantarki na ci gaba da hana bunƙasar sabis musamman a yankunan karkara, lamarin da ke barazana ga cimma burin shirin National Broadband Plan na kai kashi 70 kafin ƙarshen shekara.

Sai dai duk da haka, hauhawar amfani da data a Nijeriya na nuna gagarumar dama ga kamfanonin sadarwa da tattalin arzikin dijital baki zaya. Masana na hasashen cewa idan aka samu daidaiton farashi da cikakken goyon bayan manufofi daga gwamnati, ana iya ci gaba da kafa sabbin tarihi har zuwa shekarar 2026.

By ukarofi