
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Babban Kamfanin Man Fetur na Ƙasa NNPCL a karo na biyu cikin sati guda ya rage farashin fetur.
Jaridar ‘Daily Post’ ta ruwaito cewa a ranar Laraba aka ga gidajen man kamfanin sun rage farashin kowace lita daga N895 zuwa N890.
Hakan ya nuna an samu ragin N5 idan aka kwatanta da N895 da ake sayerwa a baya.
Tuni gidajen man a yankunan Kubwa, Gwarimpa, Wuse, da wasu wurare a Abuja suka rage farashinsu a famfuna zuwa sabon farashin.
Yayin da NNPCL ya yi ragin farashin, gidajen man da ke dako daga Matatar Ɗangote kamar su AP Ardova, Optima, MRS da Bovas suna sayerwa akan N885.
Ana ganin hakan a matsayin matakin da kamfanonin mai suka ɗauka na cigaba da ƙoƙarin rage farashin fetur a faɗin Nijeriya, kamar yadda Shugaban Ƙungiyar ƴan Kasuwar Fetur masu Zaman kansu ta Ƙasa, Abubakar Maigandi ya bayyana wa manema labarai a kwanakin baya.
