
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’annati (EFCC) ta kama mutane 25 bisa zargin su da hannu a ayyukan damfara ta yanar gizo a Kano.
Kakakin hukumar, Dele Oyewale a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba a Abuja, ya ce an kama mutanen ne a yankin unguwar da ke daura da sabon sashin Jami’ar Bayero (BUK), wato New Campus.
Ya ce, “baki ɗaya waɗanda ake zargin ɗalibai ne da ke karatun digiri a BUK.”
Ya kuma ce, daga cikin ababen da aka ƙwato a hannun ɗaliban akwai wayoyin hannu, kwamfotocin ‘laptop’, na’urorin sadawar intanet da wata mota ƙirar Honda Accord.
Oyewale ya bayyana cewa, hakan ya biyo bayan nazari na makonni da jami’ai suka yi a yankin bisa zargin wasu da ke ayyukan nau’ukan damfara da dama ta intanet.
Kazalika, ya ce za a miƙa su ga kotu da zarar an kammala bincike akan su.
