
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Gwamnatin Jihar Yobe tare da haɗin-gwiwar hukumomin tsaro sun yi nasarar sake buɗe kasuwannin Kukareta da Buni-Yadi, waɗanda aka rufe su a baya sakamakon matsalolin rashin tsaro da yankunan suke fuskanta.
An rufe kasuwannin, waɗanda ke Ƙananan Hukumomin Gujba da Damaturu ne domin rage damar samar da abinci ga mayaƙan ƴan ta’adda da ke addabar al’umma a ƴan kwanakin nan.
Mai bai wa gwamnan jihar, Mai Mala Buni Shawara kan Harkar Tsaro, Dahiru Abdulsalam ya shaida wa manema labarai hakan jim-kaɗan bayan kammala zama akan lamuran tsaro a ƙarƙashin jagorancin Mataimakin Gwamnan, Barde Gubana a Gidan Gwamnati dake Damaturu a ranar Laraba.
Ya ce, an ɗauki matakin ne bayan nazari game da hali tsaro a sassan jihar.
Abdulsalam ya bayyana cewa, dokar hani da aka yi akan sayer da man fetur daga ƙarfe 6 na yamma zuwa 6 na safe tana nan daram.
Haka kuma Mai bai gwamnan shawarar ya ƙara da cewa, gwamnatin jihar za ta samar da jami’ai na musamman domin kula da lamuran manoma da makiyaya ta yadda za su tabbatar ba a samu tsokanar juna a tsakanin ɓangarorin biyu ba duba yadda hakan ke haddasa rikici a tsakanin su a baya.
