NNPP ta yi wa siyasata ƙanƙanta, inji Farouk Lawan

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Tsohon ɗan Majalisar Wakilai kuma wanda ya samu yafiyar shugaban ƙasa a kwanan nan, Farouk Lawan, ya bayyana jam’iyyar NNPP a matsayin wadda ta yi wa siyasarsa ƙanƙanta, inda ya ce an fi saninsa da tafiyar siyasar da ta shahara a mataki na ƙasa.

A wata hira da shi da BBC Hausa ranar Talata, Farouk Lawan ya ce ya fi ra’ayin haɗa hannu da jam’iyyu masu ƙarfi a mataki na ƙasa, a cewarsa, NNPP a Kano ma ba ta gama samun karɓuwa a wajen al’umma ba duk da cewa ita ke mulki a jihar.

Ya kuma yi tsokaci akan ƙalubalen da ya fuskanta a shekarun baya zuwa yanzu musamman zamansa a kurkuku, inda ya samu horo akan halin ɗan-adam, biyayya da alaƙar siyasa.

“Idan Allah ya sa ka shiga jarrabawa, sai kuma ya buɗe maka idanu domin ka ga su wanene asalin abokan tafiyarka”, inji shi.

Tsohon ɗan majalisar ya kuma zargi mambobin tafiyar Kwankwasiyya, waɗanda da yake tare da su da yasar da shi a lokacin da ake shari’arsa.

Ya ƙara da cewa, har yanzu akwai ɗaya daga jiga-jigan tafiyar da bai kira shi domin taya murnar fitowa daga gidan yari ba bayan shekara guda da hakan.

Kazalika, Lawan, wanda ya wakilci mazaɓar Ɓagwai/Shanono ta Jihar Kano, yana ɗaya daga cikin mutane 175 da suka samu yafiyar shugaban ƙasa ƙarƙashin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu a kwanan nan.

A shekarar 2021 aka yanke masa hukunci akan laifuka uku masu alaƙa da rashawa bayan zargin sa da karɓar cin hanci tun a 2012.

Akan haka aka yanke masa hukuncin shekara bakwai a gidan yari. Bayan ya kammala karɓar hukuncin nasa, ya shaƙi iskar ƴanci a 2024.

By Babaji